Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 17:26:39    
Bayani game da shiyyar kudu maso yammacin lardin Guizhou

cri

Shiyyar kabilun Buyi da Miao ta kudu maso yammacin lardin Guizhou mai cin gashin kanta tana yankunan dake hada lardin Guizhou da na Yunnan da jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta ta kasar Sin. A kan tarihi, wannan shiyya ce da aka yi sufurin kayayyaki da cibiyar yin ciniki a tsakanin wadannan larduna uku. Fadin yankunan shiyyar ya kai murabba'in kilomita dubu 16 da 804. Jimlar mutanen da suke da zama a shiyya ya kai miliyan 3 da dubu 117, inda ake kunshe da kabilu 33 ciki har da Han da Buyi da Miao da Yi da Hui. Yawan mutanen kananan kabilu da suke zama a shiyyar ya kai 42.47% bisa na dukkan yawan mutanen shiyyar. An kafa wannan shiyar kabilun Buyi da Miao ne a ran 1 ga watan Mayu na shekarar 1982 wadda ke kunshe da gundumomi 8 da wata unguwar raya tattalin arziki. Babban birnin shiyyar shi ne birnin Xingyi.

Yankunan yamma da arewacin shiyyar sun yi sama, amma yankunan da ke gabas da kudancin shiyyar sun yi kasa. Ana jin dadin yanayin wannan shiyyar a duk shekara. Matsakaicin zafi na shiyyar yana tsakanin 13.6?da 19.1?. Haka kuma ana da isashen ruwan sama a shiyyar. Ana kuma ruwan sama a lokacin zafi. Ana kuma kiran wannan shiyya "dakin dumi-dumi ne na halittu" na duk shekara. Irin wannan yanayin zafi yana dacewa da noman hatsi iri iri da amfanin gona mai arziki da itatuwa.

Bugu da kari kuma, ana da wadatattun albarkatun halittu a shiyyar, kamar su kwal da man fetur da man gas da zinariya da karfe da zinc da dai sauransu. Yawan zinariya da aka gano zai kai ton 500 a nan gaba, amma yanzu yawan zinariya da aka riga aka tabbatar a shiyyar ya kai ton 208. Ana da zinariya a cikin dukkan gundumomin shiyyar. Sabo da haka, kungiyar zinariya ta kasar Sin ta nada ta matsayin "shiyyar zinariya ce ta kasar Sin". A waje daya kuma, ana da tsire-tsire da shuke shuke iri iri a shiyyar. Yawan gandun daji da aka shimfida a shiyyar ya kai 40.44% bisa na duk fadin shiyyar. Yawan itatuwa masu daraja da aka samu a shiyyar ya kai fiye da 20. Haka kuma, shiyyar na daya daga cikin wuraren da ke da wadatattun magungunan ganyaye iri iri. Ban da wadannan kuma, wannan shiyya tana da wadatattun albarkatun ruwa. Wani muhimmin sashe ne na dam mai samar da wutar lantarki da aka gina a kan kogin Honghe. Wannan dam yana kan matsayi na uku a cikin dam mafi girma a kasar Sin. Shiyyar kabilun Buyi da Miao ta kudu maso yammacin lardin Guizhou ita kuma muhimmin wuri ne da ke sufurin wutar lantarki zuwa yankunan gabashin kasar Sin. Yawan kwal da aka gano ya kai ton biliyan 19.6.

Bugu da kari kuma, ana da wuraren yawon shakatawa da yawa a shiyyar, kamar su babban kwarin kogin Maling da tafkin Wanfeng da gandun daji na Wanfeng inda ke nune-nunen labarin kasa na musamman irin na Karst.

Kamar yadda 'yan kabilun Miao da Dong suke murnar bukukuwa iri iri, 'yan kabilar Buyi da ke zama a shiyyar suna kuma murnar bukukuwa iri daban daban.

Ana iya samun saukin zirga-zirga a shiyyar kabilun Buyi da Miao ta kudu maso yammacin lardin Guizhou. Hanyar dogo da ta sada birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang da birnin Kunming na lardin Yunnan da hanyoyin mota masu lamba 324 da ta 320 da Zhensheng da Guanxing sun ratsa wannan shiyya. Bugu da kari kuma, akwai filin saukar jirgin sama a garin Xingyi. Yanzu shiyyar kabilun Buyi da Miao ta kudu maso yammacin lardin Guizhou ta riga ta zama wani kyakkyawan wurin yawon shakatawa da ke da makoma mai kyau. (Sanusi Chen)