Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 17:25:41    
Bayani game da shiyyar kabilun Miao da Dong mai cin gashin kanta da ke kudu maso gabashin lardin Guizhou

cri

Shiyyar kabilun Miao da Dong mai cin gashin kanta tana kudu maso gabashin lardin Guizhou. A gashinta shi ne birnin Huaihua na lardin Hunan, kuma a kudancinta shi ne birnin Laibing da birnin Hechi na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta ta kasar Sin. Kuma tana makwabtaka da shiyyar kudancin lardin Guizhou a yamma. Fadin wannan shiyya ya kai murabba'in kilomita dubu 30.3, kuma tana da mutane miliyan 4 da dubu 312. Yawan mutanen kabilun Miao da Dong da Buyi da Shui da Yao da Zhuang ya kai kashi 80.6% daga cikin duk yawan mutanta, daga cikinsu kuma yawan mutanen kabilar Miao ya kai 41.4%, yawan mutanen kabilar Dong ya kai 31.5%. Sabo da haka yawan mutanen kananan kabilu da yawan mutanen kabilun Miao da Dong sun fi yawa a cikin dukkan shiyyoyin kabilu masu cin gashin kansu 30 na duk kasar Sin, kuma.

Shiyyar kabilun Miao da Buyi da ke kudu maso gabashin lardin Guizhou tana da dogon tarihi, Lokacin da kasar Sin take daular Qin, yankunan da ke cikin shiyyar ta yanzu suna karkashin ikon mulkin jihohin Qianzhong da Xiang. Kuma a lokacin da kasar Sin take daular Han, suna karkashin ikon mulkin jihar Wuling da ta Zangke. Amma a lokacin da kasar Sin take daular Qing, wadannan yankuna suna karkashin shiyyoyin Zhengyuan da Liping da Douyun da Huangping. A ran 23 ga watan Yuli na shekarar 1956, an shiyyar kabilar Miao da Dong ta yanzu a kudu maso gabashin lardin Guizhou. A karkashin wannan shiyya, akwai wani birni da gundumomi 15 tare da wata shiyyar raya tattalin arziki da gwamnatin lardin Guizhou take mulki kai tsaye. Babban birnin wannan shiyya shi ne birnin Kaili.

Yankunan shiyyar kabilun Miao da Dong mai cin gashin kanta ta kudu maaso gabashin lardin Guizhou suna shafar manyan kogunan kasar Sin guda biyu, wato kogin Yangtse da kogin Zhujiang. Tsaunin Leigong shi ne yake raba su. Sabo da haka, wannan muhimmin wuri ne da ke kare yanayin daukar sauti na wadannan koguna biyu. Manyan tsaunaku da yawa suna hada juna, tare da dimbin koguna suna ratsa wa juna. Sabo da haka, kogunan da ke cikin wannan shiyya sun fi yawa a duk fadin lardin. Bugu da kari kuma, yanayin labarin kasa na shiyyar da yake da kyaun gani sosai yana samun sauye-sauye sosai. Matsakaicin zafi na wannan shiyya ya kai 14?18.5?. A lokacin sanyi, babu sanyi sosai, kuma a lokacin zafi, babu matukar zafi sabo da a kan yi ruwan sama a lokacin zafi.

Yawan gandun daji da aka shimfida a shiyyar ya kai 49.37%. Sabo da haka, wannan shiyya muhimmin wuri ne da ke samar da gandun daji a duk kasar Sin. Ana kuma kiranta "tekun gandun daji". A cikin gandun daji na tsaunin Leigong, akwai namun daji da tsire-tsire iri daban daban.

Ban da wannan kuma, shiyyar kabilar Miao da Dong ta kudu maso gabashin lardin Guizhou mai cin gashin kanta tana da dimbin albarkatun ruwa, wato yawan karfin ruwa da aka adana a shiyyar ya kai kilowatts miliyan 2 da dubu 620. Daga cikinsu, yawan karfin ruwa da za a iya amfani da shi ya kai kilowatts miliyan 1 da dubu 720. Yanzu an riga an tsara wani tsarin samar da kuma sufurin wutar lantarki da karfin kwal da karfin ruwa a shiyyar.

Bugu da kari kuma, ana da albarkatun ma'adinai iri daban daban a shiyyar. Yanzu zuwa yanzu, an riga an gano ma'adinai iri 40.

A waje daya kuma, ana fitar da hatsi iri iri da amfanin gona da aka nomansu domin samun kudi a shiyyar. Shayin da aka noma a kan tsaunin Leishan da wani shinkafa ta kauyen Danzhan da lemo na Congjiang da akuyar Rongjiang da kananan shanu na Liping sun shahara sosai a kasar Sin.

A shiyyar kabilun Miao da Dong ta kudu maso gabashin lardin Guizhou mai cin gashin kanta, ana jin dadin kyakyawan muhalli da al'adu da wayin kai na kabilu daban daban. Wannan shiya wani wurin yawon shakatawa ne mai kyaun gani sosai a lardin Guizhou. Asusun al'adun kauyuka ta kasa da kasa ta tabbatar da cewa wannan shiyya tana daya daga cikin wuraren jin dadin al'adun kauyuka da muhallin duniya da aka fi son zaba, kuma tana daya daga cikin wuraren kiyaye al'adun kabilu 10. A gundumomin Kaili da Majiang da Taijiang da Leishan, za a iya sanin al'adun kabilar Miao kwarai. A gundumomin Liping da Congjiang da Rongjiang, za a iya sanin al'adun kabilar Dong. Kuma a wuraren da ke bakin kogin Wuyang da tsaunin Yuantaishan, za a iya jin dadin muhallin halittu. Garin Zhenyuan, wani tsohon garin al'adu ne da ya shahara a kasar Sin. Kauyen Xijiang da ke tsaunin Leishan kauyen kabilar Miao mafi girma a kasar Sin, kuma kauyen Zhaoxing na gundumar Liping wani kauyen kabilar Dong mafi girma a kasarmu. A waje daya kuma, gadar Tiansheng da ke gundumar Liping ta shahara a duk duniya. Bugu da kari kuma, za a iya kai ziyara a wurin da ke garin Liping, inda aka taba shirya taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karshen shekarar 1934, kuma za a iya kai ziyara a dakin ajiye abubuwan kabilar Dong da ke garin Tang'an da dakin ajiye abubuwan tarihi na tsohon garin Longli da bangarorin Sin da Norway suka gina tare. Haka kuma, kabilu daban daban da suke da zama a shiyyar kabilun Miao da Dong ta kudu maso gabashin lardin Guizhou mai cin gashin kanta suna murnar bukukuwa fiye da 160. Sabo da haka, ana yabawa wannan shiyya cewa "gari ne da ke bukukuwa dari" da "gari ne da ke cike da wakoki da raye-raye". Bikin waka da dimbin mutane suke rera tare da aka yaba shi cewa "waka ce daga indallahi" da wakokin Miao da rawa ta garin Taijiang sun riga sun shahara a duk duniya da wuri. (Sanusi Chen)