Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 17:18:00    
Bayani game da kabilar Dong

cri

Yawancin kabilar Dong suna zama a gundummomin Liping da Congjiang da Rongjiang da Tianzhu da Jingping da Sansui da Zhenyuan da Jianhe da Yuping da ke kudu maso gabashin lardin Guizhou da gundummomin Xinhuang da Jingxian da Tongdao na lardin Hunan da gundumomin Sanjiang da Longsheng da Rongshui na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta na kasar Sin. Yawan mutanen kabilar Dong ya kai kimanin miliyan 2 da dubu 960. Daga cikinsu, mutanen kabilar kimanin miliyan 1 da dubu dari 6 suna zama a lardin Guizhou, wato yawan 'yan kabilar Dong da ke zama a lardin Guizhou ya kai fiye da rabin duk yawan 'yan kabilar na duk kasar Sin.

Kabilar Dong tana da yarenta, amma babu haruffa, suna amfani da haruffan Sinanci. A shekarar 1958, an kirkiro haruffan harshen kabilar Dong bisa haruffan Latin, kuma ana gwada su har yanzu. Galibin 'yan kabilar Dong sun kuma iya harshen kabilar Han,wato harshen Sinanci.

Asalin kabilar Dong shi ne kabilar Baiyue da ta taba zama a nan kasar Sin yau da shekaru aru aru da suka gabata. Game da yadda ake raya zaman al'ummar kabilar Dong, har yanzu ana da ra'ayoyi 2. Sasu mutane suna ganin cewa, kafin daular Tang, wato yau fiye da da shekaru dubu 1 da suka gabata, 'yan kabilar Dong sun yi zama a cikin zaman al'umma wadda ba ta samu ci gaba ba. Tun daga daular Tang, sun shiga zaman al'ummar mulkin kama karya kai tsaye. Amma a waje daya, wasu mutane suna ganin cewa, sun taba shiga zaman al'ummar bauta. Lokacin da kasar Sin ke cikin daular Tang da ta Song, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta taba kafa shiyyar Jimi a yankunan 'yan kabilar Dong. Sannan lokacin da kasar Sin take daular Yuan da ta Ming, an aiwatar da tsarin sarkuna a yankunan 'yan kabilar Dong. A wancan lokaci, yankunan kabilar Dong suna cikin zaman al'ummar mulkin kama karya. Bayan da kasar Sin ta shiga daular Qing, wadanda suke da dimbim gonaki sun soma samun cigaban tattalin arzikinsu. Amma kafin kafuwar Jamhuriyar kasar Sin, ya kasance da kungiyoyin iyalai da yankunan kabilar Dong. Dattawa ne suka da ikon daidaita harkokin iyalansu ko kauyukansu. Bayan shekarar 1956, wato bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, bi da bi ne aka kafa shiyyoyi da gundummomi da kananan hukumomi na kabilar Dong masu cin gashin kansu a yankunan da 'yan kabilar Dong suke da zama.

Kamar 'yan kabilar Miao suke yi, muhimmiyar sana'ar da 'yan kabilar Dong suke yi ita ce aikin gona, a waje daya kuma, suna cinikin gandun daji da kiwo. Tun daga karshen karni 18 da ya gabata, 'yan kabilar Dong sun yi amfani da zirga-zirga mai sauki sun yi sufurin wasu katako da shayi zuwa sauran wurare domin sayar da su. Amma har zuwa jajibirin shekarar 1949, wato shekarar da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin, tattalin arzikin dukkan yankunan kabilar Dong sun koma baya sosai. Yanzu, sabo da ana shigar da fasahohin zamani a yankunan kabilar Dong, tattalin arzikinsu ya samu cigaba cikin sauri sosai.

Kabilar Dong tana da al'adu da ladabi iri iri. Ana yabawa yankunan kabilar Dong cewa, "garin rubutattun wakoki da teku ne da ke cike da wakoki". Wakokin da 'yan kabilar Dong suke rerawa suna kunshe da wakokin bayyana abubuwan da ake so a cikin zukatan jama'a da wakokin bayyana labaru da tatsuniyoyi da dai makamatansu. Wakokin kabilar Dong suna da dadin ji sosai. Sabo da haka, a yankunan kabilar Dong, a kan fadi cewa, "abinci yana gina jiki, amma zukata suna jin dadin wakoki". Wakokin kabilar Dong da suka shahara sosai a duk fadin duniya su ne manyan wakoki, wato "Galao" ta kabilar Dong. A cikin harshen Dong, ma'anar Ga ita ce waka, ma'anar Lao ita ce kasaita, babba, ko akwai tarihi. Launonin irin wannan waka suna shan bambanci. Mutane masu dimbin yawa suna waka tare, amma ba wanda ya ba da jagoranci. Suna rera irin wannan waka cikin 'yanci.

A waje daya, 'yan kabilar Dong suna da wakokin Pipa, wato a kan rera irin wannan waka a karkashin rakiyar launin kayan goge na Pipa, ko kayan goge na Geyi, ma'anar Geyi a cikin harshen Dong ita ce kafar shanu. Launin irin wannan waka yana da laushi, kuma ya kan bayyana yadda ake farin ciki. Bugu da kari kuma, 'yan kabilar Dong suna taka raye-raye iri iri, kamar su rawar Duoye da ta Lusheng da rawar wasa da dragon ko zaki. Rawar Duoye ita ce maza da mata da yawa suna rawa tare. Lokacin da suke taka irin wannan rawa, wani mutum ya sanya hannayensa a kan kafadar mutanen da ke makwabtaka da shi. Sakamakon haka, dukkan mutanen da suke waka tare sun girka wata da'ira, suna waka suna tafiya. Rawar Lusheng ita ma rawa ce da mutanen da suke wasa da kayayyakin busa na Lusheng suna takawa tare.

Tun daga farkon karni na 18 da ya gabata, an soma nuna wasan kwaikwayo na kabilar Dong. Na ji an ce, marigayi Wu Wencai, wani dan kabilar Dong wanda aka haife shi a shekarar 1798, kuma ya rasu a shekarar 1845 shi ne ya kirkiro irin wannan wasan kwaikwayo na kabilar Dong. Irin wasan kwaikwayo yana nune-nunen al'adun kabilar Dong sosai.

Iyalai daya na kabilar Dong suna zama tare a wani kauye. Su kan gina gidajensu a bakin kogi da ke kusa da duwatsu. A bakin kauye, a kan shuka wasu itatuwa, kuma a kan kogi, akwai wata kyakkyawar gadar da ke da rufi, sabo da haka, a kan kira irin wannan gada gadar maganin ruwan sama da iska. A cikin wani kauyen kabilar Dong, ginin da ya fi muhimmanci shi ne "ginin ganga". An gina irin wannan gini ne da katako kawai, amma ba a yi amfani da kusa ko guda ba. Irin wannan gini yana da benaye a kalla 5, wasu suna da benaye 13, kuma yana da kusurwoyi 4 ko 6 ko 8. kuma yana da wani rufi mai kyaun gani. Wannan gini alama ce ta iyalan da ke zama a wannan kauye, kuma muhimmin wuri ne da iyalai suke taro lokacin da suke tattaunawa kan muhimman harkokinsu.

Gadar maganin ruwan sama da iska da aka gina tushenta da duwatsu, amma jikinta katako ne. Bugu da kari kuma, irin wannan gada tana da wani rufi, kamar yadda ake gina gidaje.

'Yan kabilar Dong suna kuma yin tufafin da atamfar da suka saka da kansu. Launukan da 'yan kabilar Dong suke so suna kunshe da baki da launin jar garura da fari da launin shudi. Tufafin da mazan kabilar Dong suke sanya babu bambanci da na mazan kabilar Han suke sanyawa. Galibinsu suna sanyawa tufafin launin baki da kwando. Tsawon rawannin da suke sanya ya kai mita 3. A lokacin da suke halartar shagulgula, suna kuma sanya kayan ado na azurfa a kan tafufinsu. Haka kuma, tufafin da matan kabilar Dong suke sanya suna da iri iri, kuma sun fi son sanya furanni irin na azurfa da hular azurfa da dutsen wuya na azurfa da munduwar azurfa.

Matasan kabilar Dong suna da 'yancin neman soyayya. Muhimmiyar hanyar neman soyayya da samari da 'yan mata na kabilar Dong suke bi ita ce "rera waka tare, kuma bayyana wa juna soyayya a karkashin inuwar farin wata". A arewacin yankunan da 'yan kabilar Dong suke zama, a kan kira irin wanna hanya "wasa tare a kan tsauni". Bayan aiki, samari da 'yan mata su kan yi wasa tare a kan tsauni, inda suka rera wa juna wakokin soyayya. Amma a kudancin yankunan da 'yan kabilar Dong suke zama, ana kiran irin wannan hanya "zuwa wani kauye" ko "neman 'yan mata". Bisa al'adarsu, a lokacin dare, wasu 'yan mata su yi aikin dinka hannu tare a wani gida, sannan samarin da suka zo daga kauye daban su neme su da su rera wakokin soyayya tare, inda suka bayyana wa juna soyayya. Idan wani saurayi da wata budurwa suna son juna, sai dai sun mika wa juna wani kayan da ke tabbatar da kasancewar soyayya a tsakaninsu.

'Yan kabilar Dong suna murnar bukukuwa iri iri, kamar su bikin sabuwar shekara ta kabilar Dong da Ranar 3 ga watan Maris bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin da Ranar 8 ga watan Afrilu, wato bikin girmamawa shanu da Ranar sarkin gandun daji da Ranar cin sabbin shinkafa da Ranar 8 ga watan Agusta na kalandar gargajiya. A cikin yawancin kauyukan kabilar Dong, akwai wani dakin ibada na Sasui, wato sarauniya Sasui tana gaban kome a cikin idon 'yan kabilar Dong. A cikin tatsuniyar kabilar Dong, sarauniya Sasui ce ta kafa kauyukan kabilar Dong yau da shekaru aru aru da suka gabata. Ranar sabuwar shekarar kabilar Dong ita ce ran farko ga watan Nuwamba na kowace shekara bisa kalandar wata ta gargajiya ta kasar Sin, wato lokacin da aka kammala aikin gona, an soma murnar girbin hatsi. A gun wannan biki, a kan yanka kaji da agwagi da ci kifayen gishiri da danyun kifayen da aka kama. An taya murnar ranar cin sabbin shinkafa ne a watan ranar da aka zaba lokacin da shimkafa ta nuna. A gun wannan biki, da farko dai, a dafa kifi da kaji da agwagi da shinkafa tare, sannan a sanyan su a gaban zane-zanen kakanin-kakaninsu domin nuna musu girmamawa. Bayan wannan, 'yan kabilar Dong su soma rera wakoki da nuna wasannin kwaikwayo da yin wasa da shanu. Wani biki daban shi ne "ranar 8 ga watan Afrilu" , wato bikin 'yan mata. A wannan rana, dole ne dukkan 'yan matan da suka yi aure su koma gidan iyayensu, kuma su rera wakoki da yin raye-raye tare da sauran yan mata da matan 'yan uwansu. Har ma su dafa wani abinci mai suna "Ci Ba" tare. Ana dafa irin wannan abinci ne kamar yadda Hausawa suke dafa tuwo.

Bugu da kari kuma, 'yan kabilar Dong sun fi wasa da shanu. A kowane kauyen kabilar Dong, akwai wani sarkin shanun da ya kware sosai wajen wasa. A wata ranar watan Fabrairu ko wata ranar watan Agusta na kalandar gargajiya, Rana ce ta yin wasa da shanu. A wannan rana, mutane sun ihu kuma sun taka raye-raye, har su kada ganga, sarkunan shanu biyu suna fama da juna a cikin wani gonaki. Irin wannan wasa yana jawo hankulan mutane kwarai da gaske. (Sanusi Chen)