Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 17:16:50    
Bayani game da kabilar Buyi

cri

Yawancin 'yan kabilar Buyi suna zama a lardunan Guizhou da Yunnan da Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Yawan mutanenta ya kai kimanin miliyan 2 da dubu 840, yawan mutanen da suke da zama a lardin Guizhou ya kai kashi 97 daga cikin kashi dari daga cikinsu. Kabilar Buyi na daya daga cikin tsoffin kabilun da suka dade suna zama a lardin Guizhou.

'Yan kabilar suna kiran kansu Buyi. Amma domin kasancewar bambanci a wurare daban daban, lafasin wannan kalma ya sha bamban. A kan tarihi, akwai sunaye daban daban da ake kiran kabilar Buyi. Amma a kan yawancin takardun tarihi, an kira ta kabilar Zhongjia. A shekarar 1953, gwamnatin kasar Sin ta girmama wa abubuwan da 'yan kabilar suke so da sunan da suke kira da kansu, an tabbatar wa kabilar suna "kabilar Buyi".

Kabilar Buyi ta dade tana zama a lardin Guizhou. Asalin kabilar Buyi shi ne mutanen Puyue. A cikin takardun tarihi da aka rubuta, an kira kabilar Buyi da sunaye daban daban, kamar su "Yiyue" da "Yipu" da "Yiliao" da dai sauransu. A cikin sanannun litattafai biyu na kasar Sin, wato "Tarihi" da "littafin daular Han", an ce, 'yan kabilar Buyi, muhimmin karfi ne na kasar Zangke ko kasar Yelang da ke shiyyar Nanzhong a lokacin da. Yankin Luoyuedi na lokacin da, yankunan da ke bakin kogin Pan da kogin Hongshuihe, wato yankuna ne da yan kabilar Buyi suke da zama. Lokacin da kasar Sin take daulolin Chunqiu da Zhanguo har zuwa karshen daular Han ta yamma, an aiwatar da tsarin bauta a yankunan kabilar Buyi. Tun lokacin da kasar Sin take daulolin Sui da Tang, an soma aiwatar da tsarin mulkin kama karya a yankunan kabilar. A lokacin da kasar Sin take daular Yuan da Ming, sarkunan kabilar Buyi ne suke mulkin yankunansu. Tun daga lokacin daular Qing, mutanen da suke da ikon mallakar gonaki sun samu damar raya tattalin arzikinsu. A da, 'yan kabilar Buyi suna mulkin kansu da tsarin zaman al'ummar iyalai da tsarin zaman al'ummar tattaunawa da tsarin zaman al'ummar dattawa. Tun daga shekarar 1951, an soma kafa shiyyoyi da gundumomi da kananan hukumomin kabilar Buyi masu cin gashin kansu. Irin wannan tsarin siyasa ya taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki da zaman al'ummar kabilar Buyi.

Kabilar Buyi tana da yarenta. A cikin zaman rayuwar yau da kullum, su kan yi mu'amala a tsakaninsu da yaren Buyi, amma galibin mutanen kabilar sun iya harshen Han, wato harshen Sinanci.

Ana kiran kabilar Buyi kabila ce ta noman shinkafa. Noman shinkafa muhimmin tattalin arziki ne da 'yan kabilar Buyi suke yi a kullum, kuma muhimmiyar alama ce da ke bayyana al'adun kabilar tun lokacin da. Har yanzu aikin noman shinkafa muhimmiyyar sana'a ce da mutanen kabilar Buyi suke yi.

Kamar yadda 'yan kabilar Dong suke gina gidajensu, 'yan kabilar Buyi suna kuma gina gidajensu a yankunan da ke bakin kogi ko dab da tsaunuka. Yawancin iyalai suna zama tare a cikin wani kauyen da ke da gidaje goma ko fiye. Har ma a wasu manyan kauyuka, ana da gidaje fiye da dari 1 ko daruruwan gidaje. 'Yan kabilar Buyi su kan gina gidajensu da katako da duwatsu. Gidajen da suka fi bayyana al'adun kabilar Buyi su ne gidajen da aka gina da duwatsu. Siffar gidajen da suka gina da katako tana kama da na gidajen da 'yan kabilar Miao suka gina, wato irin wadannan gidaje suna da wasu kafafu tare da beneye 3 da dakuna 3. Amma a karshen bene na gida, ba a gina bango ba, sai an yi amfani da wasu katako domin kiyaye dabbobin da suke kiwo a gida. Mutane su kan kwana a dakunan da ke tsakiyar bene, kuma ana ajiye dukiyoyi a bene na uku. Idan an gina wani gini a sararin kasa, ana amfani da duwatsu. A gundumomin Anshun da Zhenning da Guanling da Puding da Liuzhi, sabo da aka fitar da duwatsu da yawa, tun daga tushe zuwa bango da rufi, dukkansu duwatsu ne. Ana kiran shi "gidan duwatsu". Ba ma kawai ana amfani da duwatsu wajen gina gidaje ba, har ma ana amfani da duwatsu wajen shimfida hanya da ganuwar kauye da gadoji da dai makamatansu. A waje daya kuma, wasu kayayyakin gida ma aka kera su da duwatsu. Wannan yana bayyana basirar 'yan kabilar Buyi sosai.

Kabilar Buyi tana da ladabi iri daban daban, kamar su tatsuniyoyi da rubutattun wakoki da karin magana da almara da wakokin jama'a da kide-kiden jama'a da wasannin kwaikwayo na jama'a. Wakokin jama'a suna kunshe da wakokin da ake rerwa a kan dutse da wakokin Langshao da wakokin shan giya da manyan wakoki da kananan wakoki da wakokin tatsuniyoyi da wakokin al'adu. Daga cikinsu, wakokin Langshao, wakoki ne da matasa suke rerawa lokacin da suke neman soyayya. Kayayyakin kida na kabilar Buyi suna kunshe da gangar tagulla da ta fata da kayan busa na Suona da na Lusheng da na Xiao da sarewa mai suna "Le You". Raye-rayen da 'yan kabilar Buyi suke takawa suna kuma da iri daban daban.

Tufafin da 'yan kabilar Buyi suke sanyawa suna da halin musamman. Yawancinsu na launin baki da shudi da na fari. Tufafin maza da na tsofaffi ba su da bambanci sosai a tsakanin wurare daban daban. Amma tufafin mata na wurare daban daban suna shan bamban sosai. Kuma sun fi son sanya furanni irin na azurfa da hular azurfa da dutsen wuya na azurfa da munduwar azurfa lokacin da suke halartar bukukuwa.

Kamar yadda matasan kabilar Dong, matasan kabilar Buyi ma suna neman soyayya cikin 'yanci. Lokacin da iyalan ango suke zuwa gidan iyayen amarya domin daukar amarya zuwa gidan ango, dole ne iyalan ango da iyalan amarya su rera wa juna wakoki, ana kiran su wakokin 'yan uwa. Da dare na ranar isowar amarya a gidan ango, ana shirya bikin rera wakokin ladan. A kan kira irin wannan biki cewa, "ana neman jakar ladan har na duk dare".

Bukukuwan gargajiya da 'yan kabilar Buyi suke tayawa suna kunshe da Ranar 3 ga watan Maris da Ranar 8 ga watan Afrilu da Ranar 6 ga watan Yuni bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin da bikin cin sabuwar shinkafa da dai makamatansu. Ranar 3 ga watan Maris bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin kasaitaciyyar rana ce ta kabilar Buyi. Tun daga wannan rana, an soma noman shinkafa. A wannan rana, ana girmamawa al'ajabi na duwatsu da na kasa da na kakanin-kakanin da al'ajabi na shinkafa, kuma suna dafa abinci mai launuka 5 da farar shinkafa. A yankunan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, matasan kabilar Buyi suna shirya bikin rera wa juna wakoki, inda dubban samari da 'yan mata suke halarta. A gun bikin, samari da 'yan mata wadanda ba su yi aure ba sun san juna kuma sun tabbatar da soyayya a tsakaninsu ta hanyar rera wa juna wakoki. (Sanusi Chen)