Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 17:15:55    
Bayani na lardin Guizhou da ke da al'adu iri iri

cri

A kan tasiwirar kasar Sin, lardin Guizhou ya kasance a kan tudu na Yunnan-Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin tamkar wani kyakkyawan ganye. Yana yamma da lardin Hunan, kuma yana arewa da jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta, a waje daya kuma, yana gabas da lardin Yunnan, amma yana kudu da lardin Sichuan da birnin Chongqing. Sakamakon haka, lardin Guizhou, wani wuri ne da ke sada arewa da kudu na kasar Sin, kuma wani muhimmin wuri ne da ake ratsawa domin zuwa yankuna tekun kudancin kasar Sin.

Lardin Guizhou, wani wuri ne da ke cike da manyan tsaunuka. A cikin yankunansa da yawansu ya kai murabba'in kilomita dubu 176.1, yawan tsaunuka ya kai kashi 92.5 cikin kashi dari. Daga cikinsu kuma yawan yankunan Karst topography ya kai kashi 61.9 cikin kashi dari bisa duk yawan fadin lardin. Sabo da haka, lardin Guizhou shi kadai ne lardi da ba shi da flatlands(sararin kasa) a nan kasar Sin. A waje daya kuma, ya fi sauran wuraren kasar Sin da na duniya kasancewar yankunan Karst topography. Sabo da ya kasance da dimbin manyan duwatsu da kwazazzabe a lardin, yana da yanayin duniya iri iri. Amma domin ya kasance da dimbin manyan duwatsu iri iri, a wannan lardi, babu sanyi sosai kuma babu zafi a duk shekara. Sakamakon haka, ya kasance da albarkatun halittu iri daban daban.

Idan ka je lardin Guizhou, mutanen Guizhou wadanda suke maraba da baki da hannu bibbiyu, za su bayyana muku a filla filla, cewar a wannan lardi, akwai Huangguoshu Grand Fall, wato faduwa ta farko a nan kasar Sin. A waje daya, a kan tarihin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ta taba shirya wani muhimmin taro a birnin Zunyi a watan Janairu na shekarar 1935, a gun wannan taro ne, aka tabbatar da matsayin Mao Tsedong da ya zama shugaban jam'iyyar. Bugu da kari kuma, lardin Guizhou ya yi suna sosai a nan kasar Sin wajen dafa giya mai zafi (wine) a garin Maotai. Sannan kuma, ya kasance da kogwanni da yawa a karkashin kasa. Kuma akwai kwarin kogin Maling, ana siffanta wannan kwari cewa, "tabo mafi kyaun gani ne da ke kasancewa a kan duniyarmu". Idan ka shiga lardin Guizhou, kamar ka shiga wani babban wurin shan iska.

Bisa nazarin da aka yi kan labarin wannan lardi, an ce, yau da shekaru miliyan 250 da 230 da suka gataba, wannan wurin da ake kiranshi Guizhou yanzu wani sashe ne da ke gabashin tekun Goodtis. Amma a wata rana, ba zato ba tsammani, kusan dukkan namun daji da ke zama a wurin da yawansu ya kai kashi 90 cikin kashi dari sun gushe a nan duniyarmu. Yanzu dai za mu iya ganin saura nasu kadai. Sakamakon haka, yanzu lardin Guizhou ya zama wani wurin da ke da dimbin fossil na yau da shekaru aru aru da suka gabata.

Amma, idan ka yi yawo a wasu wuraren yawon shakatawa na halittu kawai, ba za ka iya fadi cewa ka riga ka san dukkan lardin Guizhou ba. A lardin Guizhou, abubuwan da suka fi jawo hankulan masu yawon shakatawa, kuma mafi ban sha'awa su ne al'adu iri iri da ke kasancewa a kauyukan kabilu daban daban na lardin.

Lardin Guizhou, lardi ne da kabilu daban daban suke zama tare cikin jituwa. A cikin dukkan kabilu 56 na kasar Sin, 'yan kabilu 49 suna zama a lardin Guizhou. Daga cikinsu, 'yan kabilun Han da Miao da Buyi da Dong da Tujia da Yi da Gelao da Shui da Hui da Bai da Yao da Zhuang da She da Maonan da Mongoliya da Man da Qiang sun dade suna zama a lardin. Ya zuwa karshen shekara ta 2007, yawan mutanen lardin Guizhou ya kai kusan miliyan 40, daga cikinsu yawan 'yan kananan kabilu ya kai kusan kashi 39 cikin kashi dari bisa na dukkan yawana mutanen lardin. A waje daya, mutanen kabilun Buyi da Shui da Gelao da yawansu suka kai fiye da kashi 95 cikin kashi dari bisa na dukkan mutanensu da ke zama a nan kasar Sin suna zama a lardin Guizhou tare da rabin yawan mutanen kabilun Miao da Dong na kasar Sin suna zama a lardin Guizhou.

A da, sabo da lardin Guizhou yana nesa da cibiyar kasar Sin, a kan kira wannan wuri "shiyyar da ke bakin iyakar kasar Sin" ko "jihar da ke bakin iyakar kasar Sin". Tun daga shekarar 1413, wato lokacin da kasar Sin take daular Ming, Guizhou ya zama wani lardi daga cikin larduna 13 na kasar Sin.

Ko da yake lardin Guizhou wuri ne da ke cike da manyan tsaunuka, amma yana daya daga cikin sanannun wuraren da aka gano dan Adam na da. Bisa nazarin da aka yi, yau da kimanin shekaru dubu dari 2 da 40 da suka gabata, dan Adam ya riga ya fara zama a lardin. A cikin dogon tarihin da ya wuce, tsoffin kabilu na Baipu da Baiyue d Diqiang da Nanmai sun hada kan juna kuma sun yi zama tare da mutanen na kabilar Han da sauran kabilun kasar Sin da suka zo daga wurare daban daban a wannan wuri, kuma sun raya yankunan lardin Guizhou tare. Sabo da haka, har yanzu, ana iya sauraran tatsuniyoyi da ganin raye-raye da al'adu da tufafi da bukukuwa da ladabi na aka gada su daga kakanin-kakaninsu a kauyukana kabilu na lardin Guizhou.

Ko da yake jama'ar lardin Guizhou sun zo daga wurare daban-daban tare da al'adunsu daban daban, amma bayan isarsu a yankunan Guizhou, dukkansu sun sami wuraren da suke dacewa da yin zaman rayuwa, kuma suna musayar al'adunsu a lardin. Yanzu, a wuraren da ba su da nisa sosai a tsakaninsu, za a iya ganin cewa al'adunsu suna da bambanci kamar ya kasance da launuka iri daban daban a kan atamfa guda. Sabo da haka, a kan kira lardin Guizhou "lardi ne mai launuka iri iri", ko lardi ne da ke da dubban tsibiran al'adu iri daban daban. Kowane irin wannan tsibiri ya iya zama da kansa, amma suna kuma dogara da juna kwarai. Wannan ne al'adu na lardin Guizhou.

Ko shakka babu, a cikin idanuna mutanen da ba su taba kai ziyara a lardin Guizhou, lardi wani wuri ne da ke cike da kacici kacici, har ma an dade ba a san al'adun lardin Guizhou ba, kuma an samu bayanan kuskure game da lardin Guizhou. Idan an kwatanta shi da sauran wuraren kasar Sin, hakikanin gaskiya shi ne har yanzu lardin Guizhou bai samu cigaba sosai ba domin kasancewar mummunan dalilai iri daban daban a cikin tarihi da na labarin kasa da dai makamatansu. Mutanen lardin Guizhou sun gane cewa, lardinsu wuri ne da ba ya bakin teku ko manyan koguna ko bakin iyakar da ke tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya ba, a waje daya kuma, a cikin idon mutanen da ke zama a bakin iyakar kasa, lardin Guozhou "wuri ne da ke nesa da yankunan bakin iyakar kasa", amma a cikin idon mutanen da suke zama a yankunan da ke nesa da bakin iyakar kasa, lardin Guizhou yana kasancewa tamkar wurin da ke bakin iyakar kasa. Sabo da haka, mutanen lardin Guizhou sun sha wahala sosai wajen neman cigaba. Amma mutanen lardin ba su taba yin suka ba, sai dai sun yi namijin kokari wajen raya garinsu.

A cikin shekaru 30 da suka gabata, bayan da aka soma aiwatar da manufar bude kofar kasar Sin ga kasashen waje da yin gyare-gyare a gida, jama'ar kabilu daban-daban na lardin Guizhou sun yi kokari kuma su kan kyautata tunaninsu na neman cigaba. Mr. Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin yanzu ya taba yin aiki a lardin Guizhou ya nemi jama'ar lardin da su yi kokari kan yadda za a iya samun babban cigaban tattalin arziki da zaman al'ummar lardin cikin sauri. Bisa wannan bukatar da Mr. Hu yake nema cimmawa a lardin, gwamnati da jama'ar lardin Guizhou sun tsara shirin neman bunkasuwar lardin bisa halin da ake ciki a lardin tare da kiyaye yanayin duniyarmu domin kokarin neman cigaban tattalin arziki da zaman al'umma a lardin da kyau kuma da sauri. A cikin shekaru 5 da ke tsakanin shekara ta 2002 da ta 2007, matsakaicin saurin cigaban tattalin arzikin lardin ya kai 11.7% a kowace shekara. An kuma daidaita dimbin matsalolin da suke da nasaba da zaman rayuwar fararen hula. Ingancin zaman rayuwarsu ya samu kyautatuwa cikin sauri. Ayyukan yau da kullum na lardin sun kuma samu karfafuwa. A waje daya kuma, an mai da hankali sosai wajen tabbatar da ingancin muhalli na lardin Guizhou lokacin da ake neman bunkasuwa.

Domin lardin Guizhou yana da wuraren yawon shakatawa masu kyaun gani sosai, a lokacin da jama'ar lardin suke neman ci gaban tattalin arziki da kyautata zaman rayuwarsu, su mai da hankali sosai wajen yin amfani da irin wannan kyakkyawan yanayin halittu. A tsakanin shekara ta 2005 da ta 2007, an shirya dimbin bukukuwa masu take "lardin Guizhou mai launuka iri iri" a fannonin gasannin rera wakoki da raye-raye na kabilu da kuma zabar kyakkyawar yarinya domin kara wa sauran wuraren duniya sanin lardin Guizhou. Yanzu, ba ma kawai ana ta sanin sabon lardin Guizhou a nan kasar Sin ba, har ma ana sanin shi a duk fadin duniya.

Al'adu iri daban daban suna kasancewa tare a nan duniyarmu, kabilu daban daban na lardin Guizhou ma suna kokarin koyon al'adun sauran yankunan duniya. Sabo da kabilu daban-daban na lardin Guizhou sun iya yin koyi da juna sosai, zuriyoyin kabilu daban daban sun iya zama tare cikin lumana a cikin dogon lokacin da ya gabata. Wannan ya riga ya zama al'adar bai daya ta kabilu daban-daban na lardin. Kuma yana bayyana cewa, lardin Guizhou lardi ne da ake samun jituwa a tsakanin kabilu daban daban, kuma a tsakanin dan Adam da muhallin duniyarmu. (Sanusi Chen)