Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 16:11:08    
Sanannun 'yan wasan motsa jiki na Amerika suna sa ran alheri ga gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Rahotanni daga kafofin yada labarai na kasar Amerika sun ce, kwanan baya a wajen taron ganawar kafofin watsa labarai da 'yan wasannin motsa jiki na Amerika wadanda za su halarci gasar wasannin Olympics ta Beijing, mashahuran 'yan wasan motsa jiki na Amerika da dama sun sa ran alheri ga gasar wasannin Olympics ta Beijing wadda za'a shirya nan ba da jimawa ba.

A gun ganawar, 'yar wasan kwallon kafa wadda ta fi kwarewa a harbar kwallo a raga ta kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta Amerika Abby Wambach ta ce, burinmu shi ne a yi iyakacin kokarin halartar gasanni a madadin Amerika, tare kuma da yadada ra'ayin shimfida zaman lafiya a duniya da gasar wasannin Olympics.

"Nuna bijirewa ga kyakkyawar ma'anar gasar wasannin Olympics da wasu mutane suka yi ya bakanta mini rai," in ji wata sananniyar 'yar wasan kwallon kafa daban ta kungiyar Amerika mai suna Heather O'Reilly.

Michael Phelps, shahararren dan wasan ninkaya wanda ya samu lambobin zinariya guda 6 na gasar wasannin Olympics ya fadi cewar, "Na kai ziyara sau da dama a Beijing, na ga mutane suna farin ciki sosai. Shekarar da muke ciki shekarar gasar wasannin Olympics ce, shi ya sa ina fatan zage damtse domin halartar gasar wasannin Olympics a Beijing."

Bayan ganawar, Jaridar World Journal ta Amerika ta bayar da wani rahoto dangane da wannan taro. Rahoton ya ce, wasu kafofin yada labarai na Amerika sukan saka batun siyasa a gasar wasannin Olympics. Amma burin da 'yan wasannin motsa jiki suke kokarin neman cimmawa shi ne yin mu'amalar motsa jiki, da halartar gasanni, da kare mutuncin kasa da mutane su kansu. Ba su fatan a yi karan-tsaye ga gasar wasannin Olympics ta hanyar saka batun siyasa, haka kuma ba su fatan ganin cewa kokarin da suka yi cikin shekaru da dama ya zama abin banza.(Murtala)