Da safiyar yau 21 ga wata din nan ne, shugaban majalisar dattawa na kasar Faransa wanda a yanzu haka yake ziyara a nan kasar Sin Christian Poncelet ya isa filin jirgin sama na Pudong na birnin Shanghai. Da saukarsa bai zame ko'ina ba sai cibiyar motsa jiki ta nakasassu ta Shanghai, a wata ziyarar musamman da ya kai ga wata mai dauke da fitilar gasar wasannin Olympics mai suna Jinjing, kuma ya isar da wasikar nuna juyayi daga wajen shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa zuwa gare ta.
Jinjing wata nakasasshiya ce mai dauke da fitilar gasar wasannin Olympics ta Beijing. Tsirarrun 'yan a-ware masu neman 'yancin kan Tibet sun kai mata hare-hare yayin da take yawo da fitilar gasar wasannin Olympics a ranar 7 ga watan da muke ciki a birnin Paris na kasar Faransa.(Murtala)
|