Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 14:58:58    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Mun samu labari daga kwamitin harshen Tibet na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin cewa, a halin yanzu a dukkan lokutan koyon ilmi wato makarantun firamare da sakandare da kuma jami'a, ana ba da ilmin harshen Tibet ga 'yan makarantun jihar, musamman ma ga 'yan makarantu 'yan kabilar Tibet.

Jihar Tibet ta kaddamar da dokokin musamman domin kawo tabbaci ga yin karatu da yin amfani da kuma bunkasa harshen Tibet, an tsai da cewa, dole ne 'yan makaranta 'yan kabilar Tibet na makarantu daban-daban su mai da harshen Tibet a matsayin muhimmin darasi. Kuma dukkan makarantu firamare su ba da ilmi ga yaran kabilar Tibet da harshen Tibet, makarantun sakandare da kolejoji da jami'o'i kuma su mai da harshen Tibet a muhimmin matsayi wajen karatu. Kuma dole ne 'yan makaranta na kabilar Han su mai da harshen Tibet a matsayin darasi tilas a lokaci mai dacewa.

---- Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta juya hankalinta daga birane da garuruwa zuwa shiyyoyin noma da kiwon dabbobi wajen matakan da ta dauka da kuma kudin da ta ware domin ba da gudummawa ga jihar Tibet, ta yadda zaman rayuwar manoma da makiyaya na jihar Tibet ya samu kyautatuwa sosai.

Yawan manoma da makiyaya ya wuce kashi 80 cikin 100 bisa dukkan mutanen jihar. Tun shekarar 2006 zuwa yanzu, jimlar kudin da jihar Tibet ta ware domin tsugunar da manoma da makiyaya ta wuce kudin Sin wato Yuan biliyan 1.7, daga cikin kudaden fiye da Yuan biliyan 3 da za a ware cikin shekaru 3 masu zuwa domin ba da gudummawa ga jihar kuma, yawancinsu za a yi amfani da su ne domin sa kaimi ga aikin tsugunar da mayawata masu kiwo, da daukar mutane masu yaki da kangin talauci zuwa sabbin gidaje, da kuma kyautata lalatattun gidajen manoma, ta yadda zuwa shekarar 2010, za a yi kokarin daukar manoma da makiyayya fiye da kashi 80 bisa 100 na jihar Tibet cikin gidaje masu inganci, kuma za a rubanya kokari domin yin muhimman gine-gine, da kara saurin bunkasa harkokin ba da ilmi da kiwon lafiya da al'adu.

Daga shekarar 1995 kasar Sin ta fara ba da gudummawa ga jihar Tibet tsakanin sassan da abin ya shafa, wurare daban-daban na duk kasar sun ware kudi domin ba da taimako ga jihar. Bisa ci gaban da aka samu wajen ba da gudummawa ga jihar Tibet, yawan karuwar tattalin arziki da jihar ta samu cikin shekaru 7 a jere ya wuce kashi 12 bisa 100 a kowace shekara, yawan tsabar kudin da kowane manomi da makiyayi ya samu cikin shekaru 5 a jere ya karu da fiye da kashi 10 bisa 100 a kowace shekara.(Umaru)