Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 14:58:02    
Yadda aka girmama zakaru a gun gasar wasannin Olympic ta zamanin da

cri
A gun gasar wasannin Olympic a zamanin yau, dukan wadanda suka zama lambawan sun iya samun lambobin zinariya. To, mene ne wanda ya sami nasara ya samu a gun gasar wasannin Olympic ta zamanin da? Yanzu bari mu yi hira kan wannan fanni.

A gun gasar wasannin Olympic ta zamanin da, zama zakara makasudi ne kawai da dukan 'yan wasa suka nemi cimmawa. Bayan da zakaru suka dawo garinsu, a kan yi maraba da su kamar yadda aka yi maraba da jarumai. Irin wannan lambar yabo a fannin tunani ta kasance muhimmin dalilin da ya sa 'yan wasa na kasar Girka ta zamanin da ba su ji tsoron rasa rayukansu ba, sun yi iyakancin kokari domin zama zakara.

A cikin dukan shirye-shirye na gasar wasannin Olympic ta zamanin da, zakaru sun iya samun matukar girmamawa daga mutane a Girka ta da. Ba dan wasa kawai ba, har ma iyayensa da daular da yake zama dukansu sun iya samun girmamawa sosai. A zukatan mutanen Girka, wadanda suka zama zakaru a gun gasar wasannin Olympic, jarumai ne da gunkin Zeus ya fi kaunarsu, haka kuma mazauna ne masu nagarta a Girka, shi ya sa a ganin dukan wadanda suka shiga gasar wasannin Olympic, zama zakara makasudi ne a gare su. A can da, mutanen Girka sun nuna jaruntaka, sun yi gwagwarmaya domin samun nasara a cikin gasanni da kuma yake-yake.

A gun gasar wasannin Olympic ta zamanin da, sai zakara ne kawai, babu sauran lambobin yabo da aka bai wa 'yan wasa, bayan gasar, ba a nuna sha'awa ga makomar wadanda suka sha kaye ba. Shi ya sa wasu 'yan wasa ba su ji tsoron rasa rayukansu ba domin zama zakaru. Zakaru sun iya samun kambi da aka saka da rassan icen zaitun a matsayin wata kyauta. A gun gasar wasannin Olympic ta Athens a shekarar 2004, mun iya ganin ko wane dan wasa da ya sami lambobin yabo ya sanya wani kambi irin na rassan icen zaitun a kai. A farkon lokacin da ake yin gasar wasannin Olympic a zamanin da, mahukuntan dauloli na Girka sun fi dora muhimmanci kan bai wa zakaru girmamawa, kamar sassaka mutum-mutumi ga zakaru domin mutane sun iya ganinsu da nuna musu girmamawa, ko kuma ba su damar shugabantar bukukuwan addini. Amma saboda kyautatuwar matsayin zakaru, a karshen lokacin da ake yin gasar wasannin Olympic a zamanin da, an soma bai wa zakaru abubuwan kyauta da kuma ikon musamman.

Domin tunawa da wadannan zakaru har abada, shi ya sa bayan gasar wasannin Olympic ta zamanin da, a yankin gidajen ibada na Olympic, an yi mutum-mutumi bisa siffofin wadanda suka zama zakaru har sau 3. Da yawa daga cikin masu fasaha da suka sassaka wadannan mutum-mutumin, masu sassaka mutum-mutumi ne mafi nagarta a Girka ta zamanin da. Bugu da kari kuma, fararen hula na Girka ta zamanin da sun nuna matukar girmamawa ga wasu zakaru da suke da kyawawan jikuna a matsayin gunki.(Tasallah)