Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 14:56:02    
Gasar wasannin Olympic ta Beijing ta jawo hankali sosai a gun taron baje-koli kan tafiye-tafiye na kasa da kasa a kasar Sin

cri
A kwanan baya, an yi taron baje-koli kan tafiye-tafiye na kasa da kasa na shekarar 2008 a birnin Zhengzhou, babban birnin lardin Henan na kasar Sin. 'Yan kasuwa da suka halarci taron sun nuna ababen yawon shakatawarsu daga fannonin al'adu da tarihi da sigogin musamman na kananan kabilu da ni'imtattun wurare da dai sauransu. Ababen yawon shakatawa domin gasar wasannin Olympic ta Beijing sun fi jawo hankali sosai a gun taron.

A watan Agusta na wannan shekara, za a yi gasar wasannin Olympic ta karo na 29 a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, wadda take kasancewar kyakkyawar dama ga kasar Sin da ta raya sha'anin yawon shakatawa. A gun taron baje-koli da aka yi a wannan karo, dimbin 'yan kasuwa da suka halarci taron sun gabatar da ababin yawon shakatawa domin gasar wasannin Olympic ta Beijing domin jawo hankulan masu yawon shakatawa na gida da na waje. Mr. Zhu Shanzhong, jami'in hukumar aikin yawon shakatawa ta kasar Sin, wadda ta sami bakuncin shirya taron baje-kolin, ya bayyana cewa,'A karshen shekarar bara, hukumar aikin yawon shakatawa ta kasar Sin ta tabbatar da shekarar 2008 da ta kasance shekarar yawon shakatawa game da gasar wasannin Olympic ta kasar Sin. Sa'an nan kuma, hukumomin aikin yawon shakatawa na birane da larduna na kasar su ma sun dora muhimmanci kan rangadin gasar wasannin Olympic, sun shirya harkoki iri daban daban domin yada gasar wasannin Olympic. Ban da wannan kuma, hukumarmu ta wallafi littattafan ja-gora kan hanyoyin da aka tsara wa masu yawon shakatawa game da gasar wasannin Olympic, mun yi shirin rarraba su a kauyen wasannin Olympic, ta haka dukan 'yan wasa na duk duniya masu halartar gasar wasannin Olympic ta Beijing da kuma iyalansu za su san wadannan hanyoyi. Mun kuma karfafa gwiwar karin 'yan wasa da su yi bulaguro a sauran wuraren kasarmu, mun kaddamar da ziyara ta kwanaki 3 ko 4 ko 5 ko kuma 10.'

A cikin dukan 'yan kasuwa masu halartar taron, ababin yawon shakatawa domin gasar wasannin Olympic da Beijing da biranen da suke ba da taimako wajen shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing suka gabatar sun fi jawo hankulan mutane. Madam Yu Yonghui, jami'ar kula da harkokin yawon shakatawa ta hukumar gundumar Huaiyou ta Beijing ta yi karin bayani da cewa,'Masu yawon shakatawa za su iya ziyarar wuraren yawon shakatawa na aikin gona, inda za su iya cire 'ya'yan itatuwa ko amfanin gona da kuma kara fahimta kan al'adun gargajiya na kasar Sin. A sa'i daya kuma, mun gabatar da wasu hanyoyin musamman, kamar ziyarar babbar ganuwa ta kasar Sin, wato Great Wall da ziyarar kauyukan 'yan kabilar Man da dai sauransu.'

Za a yi gasar wasan kwallon kafa ta wasannin Olympic ta Beijing a birnin Shenyang na lardin Liaoning da ke arewa maso gabashin kasar Sin. Ying Zhongyuan, jami'in hukumar aikin yawon shakatawa ta lardin Liaoning, ya yi bayani da cewa,'Biranen da ke kewayen Shenyang za su nuna kyan gani irin na birane na zamani. Sa'an nan kuma, za mu jagoranci masu yawon shakatawa daga Shenyang zuwa birnin Dandong domin kallon ni'imtattun wuraren da ke bakin iyakar kasar Sin. Haka kuma, masu yawon shakatawa za su iya ziyarar bankin rairayi na teku a birnin Dalian daga birninmu na Shenyang.'

Ababin yawon shakatawa game da gasar wasannin Olympic ta Beijing su ma sun jawo hankulan dimbin 'yan kasuwa masu halartar taron na ketare. Mr. Robert Assl, jami'in kula da harkokin yawon shakatawa da tattalin arziki na hukumar birnin Berlin na kasar Jamus, wanda ya zo Zhengzhou ne domin halartar wannan taron baje-koli, ya nuna cewa, a shekarar da muke ciki, birninsu na Berlin zai inganta hadin gwiwa a tsakaninsa da kasar Sin a harkokin yawon shakatawa. Ya ce,'Na taba kawo wa kasar Sin ziyara yau da shekaru 15 da suka wuce. A cikin shekaru 15 da suka gabata, kasar Sin ta sami manyan sauye-sauyen da ba a iya kiyasta ba. Birninmu na Berlin yana tuntubar kasar Sin a harkokin yawon shakatawa sosai. Yanzu bangarorin 2 sun kaddamar da wasu shirye-shiryen yin hadin gwiwa a fannin sha'anin yawon shakatawa. Shekarar bana shekara ce ta wasannin Olympic. Za mu ci gaba da daukaka yin hadin gwiwa tare da bangaren Sin a fannoni daban daban. A shekarar da muke ciki, shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta ba da taimako mai yakini wajen raya sha'anin yawon shakatawa na kasar Sin. Karin mutanen kasar Jamus suna nuna sha'awa sosai kan kawo wa kasar Sin ziyara.'

To, masu sauraro, bayanin musamman da muka shirya muku game da gasar wasannin Olympic ta Beijing ka nan, bayan da muka dan huta kadan, zan mu kawo muku wasu abubuwa game da wasannin Olympic.(Tasallah)