Malam Mochizuki Hideaki mutumin kasar Japan ne, yanzu kuma shi ne mataimakin babban manaja na babban kamfanin hada magunguna na kasar Japan da ake kira Astellas a kasar Sin. Ya yi shekaru biyu yana aiki a birnin Shenyang, fadar gwamnatin lardin Liaoning da ke arewa maso gabashin kasar Sin. Yayin da yake hira da wakilin rediyonmu, ya ce, birnin Shenyang wani babban birni ne, ya saba da aiki da zamansa a birnin cikin sauri, kuma yana kaunarsa kwarai. Yanzu, ya riga ya mayar da birnin kamar gidansa.
A karkashin shugabancin Malam Mochizuki Hideaki, kamfaninsa ya sami bunkasuwa cikin sauri a shekarun nan da suka wuce. Yawan kudin da kamfaninsa ya samu daga wajen sayar da magungunan sha ya karu daga kudin Sin Yuan miliyan 200 a shekarr 2006 zuwa Yuan biliyan 600 a yanzu. Amma Malam Mochizuki Hideaki ya bayyana wa wakilinmu cewa, yayin da ake bunkasa harkokin kamfani, bai kamata a nemi cin kudin riba kawai ba. Bisa matsayinsa na daya daga cikin shugabanni masu kula da wani kamfanin hada magungunan sha, yana mai da hankali sosai ga harkokin kiyaye muhalli, don haka kamfaninsa yana hada magunguna ne ba tare da gurbata muhalli ba. Da Malam Mochizuki Hideaki ya tabo magana a kan wannan, sai ya ce, "ko kusa, kamfaninmu bai taba gurbata muhalli ba a cikin sama da shekaru 10 da suka wuce tun bayan kafuwarsa. " An ce, ya zuwa yanzu, kamfanin Astellas ya riga ya kashe kudin Sin miliyoyin Yuan wajen dasa ciyayi don kyautata muhalli. Haka kuma ana amfani da kayayyakin aiki na musamman don tace gurbataccen ruwa da hayakin da kamfanin ke fitarwa kafin a zubar da su. Sa'an nan kamfanin yana amfani da gurbataccen ruwan da yake tacewa wajen kiwon kifaye da yi wa filayen ciyayi ban ruwa. Nauyin ruwan da yake tsimi ya kan kai tan dubu 20 a ko wace shekara. Bisa kyakkyawan sakamakon da kamfanin ya samu wajen kiyaye muhalli, an sha ba shi lambobin girmamawa ta kiyaye muhalli.
Malam Mochizuki Hideaki ya kuma gaya wa wakilinmu cewa, yana fatan kamfaninsa zai kara fitar da sabbin magunguna masu yawa don kara warkar da masu cuta a kasar Sin. Ya kara da cewa, "ina son in yi kokari sosai wajen kara kula da kamfaninmu da kyau, ta yadda za mu kara bunkasa kamfaninmu cikin sauri. Ina da babban buri da kyawawan ra'ayoyina, kuma na shirya sosai wajen fuskantar kalubale mai yawa."
Bayan haka Malam Mochizuki Hideaki ya ce, a cikin shekaru 2 da suka wuce, ya kan ga sauye-sauyen da ake samu a birnin Shenyang, yanzu an riga an mayar da birnin don ya zama wani birni na zamani inda jama'a ke jin dadin zamansu. Ya ce, "irin saurin ci gaban da ake samu wajen raya birnin Shenyang a cikin shekarun nan ya ba ni mamaki kwarai. Ana aikin gina manyan gine-gine a ko ina cikin birnin. Aminaina wadanda suka zo birnin Shenyang daga kasar Japan don yin harkokinsu, suka ce, birnin Shenyang yana samun sauye-sauye a ko wane lokaci. Sa'an nan wasu daga cikinsu sun ce, a hakika dai, birnin Shenyang wani birni ne mai cike da kuzari."
A yayin da Malam Mochizuki Hideaki ke ganin sauye-sauyen da birnin Shenyang ke samu a ko wace rana, kuma a wani sa'i ya kai ziyara a sauran mayan birane na kasar Sin. Bayan ziyararsa, ya jiku sosai da cewa, kasar Sin tana cike da kuzari.
Malam Mochizuki Hideaki ya taba gayyatar danginsa da kuma aminansa da yawa na kasar Japan don suka yi ziyara da yawon shakatawa a birnin Shenyang, kuma yana fatan 'ya'yansa uku ma za su sami damar zuwa birnin. Ya ce, da ya sami lokacin hutu, tabbas ne, zai kawo 'ya'yansa a birnin, ta yadda za su ganam ma idonsu zaman rayuwar jama'ar Sin. Sa'an nan yana fatan zai ba da taimakonsa wajen kara dankon aminci da ma'amala a tsakanin jama'ar kasar Sin da ta Japan.(Halilu)
|