Ran 21 ga wata, Jaridar "People's Daily" ta bayar da wani bayani, inda aka fallasa karyace-karyacen da rukunin Dalai ya yi.
Da farko, ofishin wakilan rukunin Dalai da ke kasar Australia ya bayar da "sunayen mutane 40 da suka mutu" a lamarin ta da manyan laifuffuka mai tsanani sosai da ya faru a ran 14 ga watan Maris a Lhasa. Amma ba a iya samun cikakken adireshinsu ba ko wuraren ayyukansu, kuma mutane 5 da ke cikinsu suna nan da ransu.
Na biyu, Dalai Lama ya ce wai sojojin kasar Sin sun sa tufafi kamar lama domin kirkiro wani yanayin ta da hankali da mutanen Tibet suka yi. Kuma ya gabatar da wai wani hoto mai shaidu. Bincikem da aka yi ya shaida cewa, wannan hoto an dare shi ne yayin da wadanan sojojin ke daukar fim a shekarar 2001.
Na uku, Dalai ya ce, an lalata bankuna a ran 14 ga watan Maris saboda sun "kwace kudaden da gwamnatin tsakiya ya bayar". Binciken da aka yi ya nuna cewa, maganar Dalai ba ta da shaidu ko kadan ba.
Na hudu, Dalai ya ce, yawancin kantunan da aka kone a ran 14 ga watan Maris su ne "gidajen karuwai". Binciken da aka yi ya shaida cewa, wannan ne abin shirme.
A cikin wannan rubutu, an ce, karyace-karyacen da Dalai ya yi za su cutar da mutane marasa sanin kasar Sin. An ce, yayin da aka bukaci Dalai ya yi bayyani kan karyace-karyacen da ya yi, sai ya yi shiru. Mai yiyuwa ne saboda ya yi karyace-karyace a jere, shi ya sa za a tona fuskarsa ta gaskiya ga duniya.
|