
Yau da asuba, an gudanar da wata harkar yin gudu na dogon zango a birnin Kuala Lumpur, hedkwatar kasar Malaysia domin murnar isowar fitilar wasannin Olympics na Beijing. Yau da safe misalin karfe bakwai, darurruwan mazauna birnin na Kuala Lumpur sun zo filin 'yancin kai dake da dadadden tarihi na tsawon shekaru dari domin shiga harkar " Gudun taya murnar yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008". Wadannan 'yan birnin sun taru a filin saye da tufafin dake da alamar mikar wutar yola ta wasannin Olympics na Beijing a duk duniya. (Sani Wang )
|