Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-20 20:04:55    
Kungiyar manema labaru ta kasar Sin ta bukaci CNN ta nemi gafara daga jama'ar kasar Sin a hukunce

cri

A ran 19 ga wata a birnin Beijing, wani jami'in kungiyar manema labaru ta kasar Sin ta kai suka sosai kan maganar wulakanci da mai jagora na CNN Jack Cafferty ya yi wa jama'ar kasar Sin, haka kuma wannan jami'i ya bukaci CNN da kuma Jack Cafferty da kansa da su nemi gafara daga jama'ar kasar Sin a hukunce.

A ganin wannan jami'i, tun bayan faruwar tashe tashen hankula a jihar Tibet ta kasar Sin a tsakiyar watan jiya, wasu kafofin watsa labaru na kasashen waje ciki har da CNN sun bayar da labaru da yawa ba bisa gasikiya ba. A ran 9 ga wata, a yayin da CNN take ruwaito labarai dangane da mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin San Francisco, mai jan akalar shiri Jack Cafferty ya yi maganar wulakanci kan jama'ar kasar Sin. Matakan da CNN ta dauka a 'yan kwanakin baya sun saba wa ka'idar bin gasikiya wajen watsa labaru, wannan dai ba wani aikin da wata kafar watsa labaru da ke daukar nauyin da ke bisa wuyanta ta dauka ba.

Maganar wulakanci da Jack Cafferty ya yi wa kasar Sin ta saba wa da'ar sana'ar watsa labarai, haka kuma ta bayyana kyamar da ya nuna wa kasar Sin da jama'arta.(Danladi)