Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-20 18:28:09    
Sinawa dake zaune a Turai da kasar Amurka sun yi zanga-zanga ta lumana don nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

An labarta cewa, Sinawa da kuma Sinawa 'yan kaka-gida dake zaune a birnin Paris na kasar Faransa, da birnin Berlin na kasar Jamus, da birnin Landon na kasar Burtaniya, da kuma biranen Washington da Las Angiles na kasar Amurka da dai sauransu sun yi gangami da kuma zanga-zanga cikin lumana bisa babban sikeli a jiya Asabar, agogon wurin, inda suka nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing, da nuna kin jinin mutane masu neman 'yancin kan Tiber, da nuna kiyewa ga saka siyasa cikin gasar wasannin Olympics, har da nuna fushi da yin kyamar wassu kafofin yada labarai na yammacin duniya, wadanda a kwanan baya suka bayar da labarun da suka karkata hakikanan abubuwa a game da kasar Sin.

An labarta cewa, Sinawa da Sinawa 'yan kaka-gida, da dalibai dake yin dalibci a kasar Faransa kusan dubu goma da kuma wassu aminai 'yan kasar sun yi wani taron gangami bisa wani sikeli mafi girma da ba a taba ganin irinsa ba a kasar ta Faransa cikin shekaru kusan 20 da suka gabata da zummar nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing da kuma yin tir da wassu kafofin yada labarai na Faransa bisa rashin adalci da suka nuna yayin da suke bayar da labarai a game da rikicin 3.14 a Lhasa da kuma gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Ban da wannan kuma, dubban Sinawa da dalibai dake zaune a kasar Jamus sun yi zanga-zanga bisa babban mataki a birnin Berlin. Taken zanga-zangar shi ne ' nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing da nuna kiyayya ga kafofin yada labarai bisa rashin adalci da suka nuna '.

Dadin dadawa, Sinawa da Sinawa 'yan kaka-gida dake zaune a Washington da San Fransisco da Las Angeles na kasar Amurka, da birnin Landon kuma sauran birane na kasar Burtaniya su ma sun yi wani gangami don kai kara da kuma nuna goyon baya ga gagarumar gasar wasannin Olympics ta Beijing. ( Sani Wang )