Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-19 20:06:47    
Ya kamata a nuna girmamawa ga Mr. Samaranch da dai sauran 'yan kasa da kasa masu nuna adalci

cri
A ran 19 ga wata, kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ya buga wani sharhin cewa, ya kamata a nuna girmamawa ga Juan Antonio Samaranch da dai sauran 'yan kasa da kasa masu nuna adalci.

Kuma sharhin ya ce, yayin da Mr. Samaranch, shugaba mai girmamawa na duk rayuwa na kwamitin kula da wasannin Olympics na duniya ke zantawa da kafofin watsa labarai na kasar Spain a kwanan nan, ya bayyana cewa, ba a nuna adalci ga kasar Sin ba in a yi amfani da gasar wasannin Olympics wajen nuna adawa da kasar Sin. Kuma ya yi imanin cewa, tabbas ne gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta samu nasara. Ya kamata a nuna girmamawa ga Mr. Samaranch sabo da adalcin da yake nunawa.

Ban da wannan kuma sharhin ya nuna cewa, lokacin da shugaban kwamitin kula da wasannin Olympics na duniya Jacque Rogge ke nuna cewa, a idon dukkan jama'ar duniya, bai kamata a nuna adawa da gasar wasannin Olympics ta Beijing ba, lokacin da Peter Ueberroth, shugaban kwamitin kula da wasannin Olympics na kasar Amurka ya jaddada cewa, 'yan wasan kasar Amurka za su shiga gasar, haka kuma lokacin da dukkan membobi 205 na kungiyar kwamitocin wasannin Olympics na kasa da kasa da shiyya-shiyya suke kin amincewa da a nuna adawa da gasar, da kuma yin Allah wadai da a yi amfani da siyasa wajen lalata wasannin motsa jiki, dukkansu sun samu girmamawa da aka nuna musu.(Kande Gao)