Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-18 21:44:23    
Kasar Sin ba ta nemi daliban kasashen waje da ke karatu a kasar Sin da su bar kasar Sin ba a lokacin yin gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri
A ran 18 ga wata, ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ta bayyana cewa, labarin da aka bayar, an ce, wai kasar Sin ta nemi daliban kasashen waje da suke karatu a nan kasar Sin da su bar kasar Sin a lokaci da ake gasar wasannin Olympic ta Beijing, jita-jita ce da aka baza.

A 'yan kwanakin nan, wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya sun tsara labari cewa, bangaren kasar Sin zai nemi daliaban da suke karatu a kasar Sin da su bar kasar Sin a lokacin da ake gasar wasannin Olympic ta Beijing. Game da irin wadannan labarun da aka bayar, Wang Xuming, kakakin ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ya ce, irin wadannan labaru jita-jita ne da aka tsara, ba su yi daidai da hakikanin gaskiya ba.

Mr. Wang ya ce, hukumomin gwamnatin kasar Sin ba su taba neman daliban kasashen waje da suke karatu a nan kasar Sin da su bar kasar Sin ba a lokacin da ake gasar wasannin Olympic a nan birnin Beijing. Ya kara da cewa, lokacin da ake shirya gasar wasannin Olympic da gasar wasannin Olympic domin nakasassu a nan Beijing, daliban kasashen waje da suke karatu a nan kasar Sin za su iya ci gaba da zama a nan kasar Sin, wasu daga cikinsu za su kuma yi aikin sa kai. Jami'o'in kasar Sin za su kuma ci gaba da yin hadin guiwa da musaye-musaye da takwarorinsu na kasashen waje kamar yadda ya kamata, ciki har da ci gaba da karbar daliban kasashen waje da su yi karatu a nan kasar Sin. (Sanusi Chen)