Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-18 21:41:18    
Ba zai yi hakuri da ko wace harkar neman lalata aikin mika wutar gasar wasannin Olympics ba, a cewar firayim ministan kasar Thailand

cri
A ran 18 ga wata, firayim ministan kasar Thailand Samak Sundaravej ya yi bayani a birnin Bangkok, babban birnin kasar, cewa kasar Thailand tana goyon bayan gasar wasannin Olympics ta Beijing, kuma ya ji alfahari da za a iya mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing a kasar. A waje Daya kuma, gwamnatin kasar Thailand ba za ta yi hakuri da ko wace harkar neman lalata aikin ba.

A ran nan, Mr. Samak ya yi bayani a gaban kafofin watsa labarai, cewa ba sabo da aikin mika wutar gasar wasannin Olympics wani biki ne na wasannin motsa jiki, shi ya sa ba za a iya samun ko wane dalilin lalata shi ba. Kuma ya yi imanin cewa, kasar za ta iya kammala aikin na kilomita 10 cikin nasara.

Ban da wannan kuma Mr. Samak ya ce, gwamnatin kasar ta riga ta bukaci hukumomin da abin ya shafa da su dora muhimmanci kan kungiyoyin da ke da yiyuwar shirya harkokin nuna adawa yayin da ake mika wutar. Haka kuma ya ce, game da masu adawa da suka karya ka'ida, za a dauki tsattsauran matakai. Kasar Thailand za ta nuna ra'ayinta na daukar alhaki kan wannan aikin mika wutar gasar wasannin Olympics.(Kande Gao)