Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-18 21:34:17    
(Sabunta) Hukumomi na matakai daban-daban na yankin Tibet sun taimaka wa mutanen da suka ji raunuka a tashen-tashen hankula da aka yi a birnin Lhasa a ran 14 ga watan Maris

cri

Tashe-tashen hankula da aka yi a yankin Tibet a ran 14 ga watan jiya, sun haddasa farar hula 18 sun rasa rayukansu, wasu mutane kuma sun rasa dukiyoyi da gidajen kwana. Don kara taimakawa wadannan mutane sake jin dadin rayuwarsu, kwanakin nan, gwamnatin yankin Tibet da masana'antu daban-daban da jama'ar Tibet sun samar da hidimomi iri-iri gare su, sun ba da kudin karo-karo da kayayyaki don taimaka wa mutanen wadanda suka sha wahalhalu a cikin al'amarin sake farfado da rayuwarsu.

Ya zuwa yanzu, gwamnatin yankin Tibet mai cin gashin kanta ta riga ta cika alkawarinta wajen biyan kudin jin kai da yawansu ya kai Yuan miliyan 3 ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a tashen-tashen hankulan da aka yi a Lhasa a ran 14 ga watan Maris. A sa'i daya kuma, ma'aikatar harkokin jama'a ta kasar Sin za ta aiwatar da aikin jiyya ga mutanen da suka jikkata amma ba tare da inshorar jinya a birane da kauyuka da tsarin jinya a yankin noma da makiyayya ba. Hukumomi na matakai daban daban na birnin Lhasa su ma sun kaddamar da aikin ba da kudin karo-karo ga wasu mutanen da suka jikkata.

Yanzu a sakamakon manufar taimaka wa matalauta da gwamnatin Tibet ta yi da shimfida zaman karko a cikin yankin, kasuwar Lhasa tana ci kamar yadda ta ke a da. Yawancin kantuna da aka kai musu farmaki a tashe tashen hankula da yawansu ya wuce 1300 sun riga sun bude kofa sun fara gudanar da sha'anoninsu, wasu daga cikinsu kuma ana yin gyare gyarensu ko sake gina su.(Danladi)