Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-18 16:14:40    
Wasu kafofin watsa labaru na kasashen yamma sun bayar da bayanai domin yin kakkausar suka kan yunkurin neman 'yancin kan Tibet

cri
Kwanan baya, bi da bi ne wasu kafofin watsa labaru na kasashen yamma suka bayar da bayanai, inda suka yi mummunar kushewa kan duk wani yunkurin neman 'yancin kan Tibet, da yin tunani mai zurfi kan ra'ayoyin kasashen yammacin duniya da na kafofin watsa labaru daban-daban.

Tashar Internet ta kungiyar nazarin harkokin duniya ta Canada ta bayar da wani bayani kwanan baya cewar, Amurka ce ta kulla makarkashiyar rura wutar tashin hankali a Tibet tare da zummar yiwa kasar Sin sharri. Bayanin ya ce, tunzura tsirarrun 'yan a-ware  tada tarzoma a Tibet a lokacin da za a kaddamar da gasar wasannin Olympics nan ba da jimawa ba, wani mataki ne da Amurka ta tsaurara domin kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a nan kasar Sin. Tun daga gungun mutane mabiya Dalai lama suka yi gudun-hijira zuwa Dharamsala har zuwa yau, sun samu tallafin  miliyoyin daloli daga wajen asusun dimokuradiyya na kasar Amurka wanda ke karkashin inuwar hukumar leken asiri ta CIA wanda ke samun tallafin kudi daga majalisar dokokin Amurka. Amma rahotanni daga kafofin watsa labaru na kasashen yamma dangane da tashe-tashen hankula a Tibet ba na gaskiya ba ne, kuma ba a gudanar da bincike a kansu ba. Malam Bahaushe ya kan ce, munafuncin dodo ya kan ci mai shi. Shi ya sa bayanin ya kara da cewar, duk wani yunkurin hambarar da gwamnatin kasar Sin da yiwa Beijing sharri zai ci tura!

A waje daya, yayin da wani mashahurin kwararren kungiyar harkokin diflomasiyya ta kasar Jamus kan batun Sin Eberhard Sandschneider ke zantawa da Muryar Jamus shekaranjiya 16 ga wata, ya bayyana cewar, akasarin labaran da kafofin watsa labaru na Jamus suka bayar kalaman Dalai Lama ne, abin takaici shi ne wadannan labaran da ba na gaskiya ba da kafofin watsa labaru na Jamus suka bayar tare da nufin jawo hankulan mutane ne zalla, ba su dace da hakikanin halin da ake ciki ba.(Murtala)