A ran 16 ga wata, Sinawa mazaunan kasashen waje dake jihar Minnesota na kasar Amurka sun yi zanga-zanga don nuna rashin jin dadi ga yunkurin neman 'yancin kan Tibet da Dalai Lama ke yi a wurin, da kuma fallasa abin da Dalai ke yi na zuga masu neman yancin kan Tibet da su lallata gasar wasannin Olympic na Beijing.
Bisa labarin da kanfanonin watsa labaru a wurin suka bayar, an ce, ran nan da safa, Sinawa mazaunan kasashen waje dake jihar Minnesota sama da 50 sun daga tutar kasar Sin da allunan kirari sun yi zanga-zanga a titin birnin Rochester. Sinawa da suka shiga zanga-zangar sun gaya wa kanfanonin watsa labaru cewa, sun ji fushi sosai sabo da yada jita-jita da Dalai Lama ke yi kan tarzoma dake auku a jihar Tibet, sa'I daya kuma, ba su son wadansu 'yan siyasa na Amurka da su sa hannu a cikin harkokin gida na kasar Sin.
A ran 15 ga wata kuma, Sinawa mazaunan kasashen waje da daliban kasar Sin dake birnin Seattle sun shiga zanga-zanga don shimfida zaman lafiya da aka shirya a filin wasan kwalon kwando a jami'ar Washington, don nuna rashin jin dadi ga yunkurin neman yancin kan Tibet da Dalai ke yi.
Mr. Tan Wenzhao, daya daga cikin mutane masu shiryar zanga-zangar nan ya bayyana cewa, Sinawa mazaunan kasashen waje da daliban kasar Sin dake kasashen waje sun shirya zanga-zangar da kansu ta Internet, don metanen kasar Amurka sun iya kara fahimtar abin gaskiya game da tarzoma da ta auku a jihar Tibet na kasar Sin. (Zubairu)
|