Aminai 'yan Afrika, madam Ping yali, wata makauniya ce dake da wani yaro; kuma wata ma'aikaciya ce da ta rasa aikin yi; Kazalika, wata malama ce mai aikin tausa, wadda kuma take bude shafi kan internet. Aminai masu sauraro, kila kuna tsammanin cewa ita madam Ping Yali wata nakasasshiya ce kawai, amma ina so in gaya muku cewa, ita wata Basinniya ce da ta samu lambar zinariya ta farko a gun gasar wasannin Olympics ta nakasassu.
Wata rana da sassafe, wakilinmu ya bakunce ta a nan birnin Beijing, inda a lokacin akwai sanyi kadan kuma babu hasken rana. Amma ita Madam Ping Yali mai tsananin hakiyar ido ta je ofishin aikinta bisa jagorancin kare mai suna " Lucky" domin yin aikin tausa. Ofishin aikin tausan na da tsabta sosai; kuma a kan bangon ofishin akwai wani babban hoto mai launi da ta dauka tare da tsohon shugaban hadaddiyar kungiyar kula da harkokin nakasassu ta kasar Sin Mr. Deng Pufang.
Da yake Madam Ping Yali ta samu tsananin hakiyar ido, shi ya sa take gazawa wajen duba duniya da idanunta biyu kamar yadda ya kamata tun da aka haife ta. Ta fada wa wakilinmu cewa, tun tana karama, tana sha'awar wasan motsa jiki. Ta kuma kara da cewa, a lokacin da take yin karatu a makarantar firamare, ta kware sosai wajen yin gudu. Wata rana lokacin da take yin wasan gudu tare da 'yan aji, ta yi gudu da saurin gaske har ta bar 'yan ajin baya, nan take wani malamin koyarwa ya zabe ta a matsayin 'yar wasa nakasasshiya. To, daga wannan lokaci dai, Madam Ping Yali ta jure wa tulin wahalhalu lokacin da take samun horo.
Hausawa kan fadi cewa: " Kwalliya ta biya kudin sabulu". Madam Ping ta samu sakamako mai tsoka, har ta samu wata lambar zinariya a wasan dogon tsalle na gasar wasannin Olympics ta nakasassu da aka gudanar a watan Yuni na shekarar 1984 a Los Angeles na kasar Amurka. Hayan ya karya matsayin rashin samun lambar zinariya ko daya da kasar Sin ta samu a gun gasannin Olympics na nakasassu da aka gudanar a da.
A lokacin a Madam Ping Yali ta samu lambar zinariya, ta tuna da mamarta, wadda ta rasu sakamakon cutar kansa tun lokacin da Madam Ping take da shekaru takwas kawai da haihuwa.
A shekarar 1988, Madam Ping ta dasa aya ga zaman wasan motsa jiki na tsawon shekaru 9. A duk tsawon lokacin, ta samu lambobin yabo fiye da goma. Daga baya dai ta zama wata ma'aikaciya da ta sauke daga gurbin aikinta. A lokacin, ta sha wahala sosai, ba ta da kudin kwabo ko daya, har ta bayyana nufin tallar lambar zinariya da ta samu a gun gasar wasannin Olympics ta nakasassu. Ta fada wa wakilinmu cewa : " Lokacin da nake samun horo, lokaci ne mafi kyau gare ni wajen yin karatu; amma na gaza wajen yin karatu cikin taka-tsantsan. A lokacin da nake sauka daga dandalin karbar lambar yabo, a zahiri dai na sha wahala a rayuwata. Amma duk da haka, na tuna da cewa, ban tsufa ba, bai kamata na dogara da agajin gwamnati ba. Saboda haka ne, na kuduri aniyar kago sana'a kamar sauran wassu mutane suke yi".
A ranar 29 ga watan Yuni na shekarar 1999, Madam Ping Yali ta bude wani karamin asibitin tausa bisa fasahar da ta samo daga makarantar makafi. Wani mai rashin lafiya mai suna Lin Jun na Madam Ping ya fada wa wakilinmu cewa: " Shekaru da dama ke nan Madam Ping Yali take yi mini tausa. Na gane wa idona wahalhalun da wata zakarar wasannin Olympics ta sha. Amma ba ta sunkuyar da kanta a gaban wahalhalun ba, kuma tana kokari matuka tare da nuna kyakkyawar halayya ta mai kago sana'a".
Ya zuwa shekarar dake tafe, rayuwar Madam Ping Yali ta kyautatu sosai, ta kuma bude shafin internet mai suna "Duniya mai haske ta Ping Yali" don bada kwarin gwiwa ga sauran nakasassu dake neman aikin yi. Madam Ping ta furta cewa: "Ina so in gaya wa dukkanin 'yan wasa cewa, a duk tsawon lokacin da suke samun horo, bai kamata su manta da samun karin ilmi ba. Ina fatan dukkanin 'yan wasa ciki har da naasassu su gudanar da rayuwarsu da kyau kamar yadda ake yin gudun yada kanin wani na tsawon mita dari".
|