
Ran 17 ga wata, a birnin New Delhi, hedkwatar kasar Indiya, an sami nasarar mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing.

New Delhi zango ne na 11 a kan hanyar mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a ketare. An kaddamar da aikin mikawar ne a ran 17 da wata da yamma misalin da karfe 4 da minti 45 bisa agogon wurin. An dauki awa daya da rabi wajen mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing. Tsawon hanyar mika wutar ya kai misalin kilomita 2.3 daga fadar shugaban Indiya zuwa babbar kofar Indiya. Masu rike da wutar 70 sun shiga wannan aiki, a ciki har da wasu shahararrun 'yan wasa na Indiya.
Bayan birnin New Delhi, za a ci gaba da mika wa juna wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Bangkok, hedkwatar kasar Thailand ran 19 ga wata.(Tasallah)
|