Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-17 20:26:53    
Nuna adawa da ayyukan neman 'yanci kan Tibet, abu daya ne da ke cikin zukatan Sinawan da ke zama a ketare

cri

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, rukunin Dalai ya shirya kuma ya ta da lamarin nuna karfin tuwo a ran 14 ga watan Maris a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, kuma ya aikata laifin hana mika wutar wasannin Olympic ta Beijing a kasashen duniya. Sinawan da ke zama a nan kasar Sin ko a sauran kasashen duniya sun nuna babbar hasala sosai ga ayyukan da rukunin Dalai ya yi. Kungiyoyin Sinawa da ke zama a ketare su da kansu sun taru domin tsaron wutar wasannin Olympic ta Beijing. Nuna adawa da yunkurin neman 'yanci kan Tibet da yunkurin kawo wa kasar Sin baraka abu daya ne da ke cikin zukatan Sinawan da ke zama a ketare.

A birnin London, Sinawan da ke zama a kasar Britaniya suna kada ganga a kan titin birnin London domin maraba da isar wutar wasannin Olympic ta Beijing a kasar Britaniya. A waje daya kuma, Sinawan da ke zama a kasar Faransa sun rera taken kasar Sin a lokacin da suke tsaron wutar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Paris.

Sabo da jita-jitar da rukunin Dalai ya yayafa da wasu labaru ba na gaskiya ba da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suka bayar, wasu mutanen kasashen yammacin duniya ba su da hakikanin tarihi na jihar Tibet da hakikanin lamarin nuna karfin tuwo da ya auku a ran 14 ga watan Maris. Lokacin da Sinawan da suke zama a ketare suke tsaron wutar wasannin Olympic ta Beijing cikin hadin guiwa, suna kuma bayar da ra'ayoyinsu a gun tarurruka da shafuffukan yanar gizo, sun kuma sanar wa mutanen kasashen waje hakikanin tarihi, haka kuma sun tono yunkurin kawo wa kasar Sin baraka da rukunin Dalai Lama yake yi.

"Tun yau da shekaru 700 da suka gabata, yankin Tibet ya riga ya zama wani yankin kasar Sin da ba za a iya kebe shi daga kasar ba. Abubuwan tarihi iri daban daban sun bayyana cewa, tun daga daular Yuan, aka soma hada yankin Tibet a cikin kasar Sin, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta soma mulkin yankin har yanzu. Tun daga wancan lokaci zuwa yanzu, ba a taba canja irin wannan halin da ake ciki ba, wato yankin Tibet wani yanki ne da ke karkashin mulkin kasar Sin."

Jama'a masu sauraro, wannan shi ne wani Basine da yake gaya wa masu sauraro tarihin yankin Tibet a gun wani taron da aka shirya a birnin Ottawa na kasar Canada. Sannan kuma a cikin wani shirin da gidan rediyon Faransa na biyu ya tsara, wani dalibin kasar Sin da ke karatu a kasar Faransa ya tono wa masu kallon TV karyar da rukunin Dalai ya yi game da labarin nuna karfin tuwo da aka yi a ran 14 ga watan Maris a birnin Lhasa. Ya ce, "A cikin shirye-shiryen da aka watsa dazu, wasu Lama sun ce, wato ba su ji ba su gani ba. Amma abubuwan da muka gani su ne, wasu Lama ne suka tayar da wannan lamarin nuna karfin tuwo. A waje daya kuma, wani abu mafi muhimmanci shi ne wasu Lama sun ce, wai babu lamarin zubar da jini, babu kisan gilla. Sabo da haka, ina neman 'yan gudun hijira na Tibet da su gaya wa kafofin watsa labaru hakikanan abubuwa."

A cikin jerin kwanakin da suka gabata, tun daga birnin London zuwa Paris, kuma tun daga birnin San Francisco zuwa birnin Buenos Aires, Sinawan da suke da zama a ketare su da kansu ne suka dauki matakan tsaron wutar wasannin Olympic ta Beijing da kuma nuna adawa da yunkurin neman 'yanci kan Tibet.