Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-17 17:23:50    
Wani 'dan takara daga jihar Xinjiang ta kasar Sin mai suna Kadel Kurban da ke neman mika wutar yola a wasannin Olympic na Beijing

cri

Kadel Kurban, wani 'dan sanda ne na kabilar Uygur, yana aikin binciken fasahar tsaron jama'a har shekaru fiye da goma. Bayan da aka yi zabe sau da yawa, yanzu ya riga ya zama 'dan takara na jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur, don neman zaman mutumin da ke mika wutar yola na wasannin Olympic.

Kadel Kurban yana ta aikin fasahar ayyuka har shekaru 17. Ya gaya wa wakilinmu cewa, hukumar fasahar ayyuka ita ce muhimmin sashen da aka mayar da kimiyya da fasaha zaman karfin bincike. Ya kan yin amfani da sabbin manufofin bincike, da kuma ilmin kimiyya da fasaha kan aikinsa, har ma ya murkushe miyagun ayyuka masu tsanani, da kuma shari'o'in ta'addanci a jere.

Iyalin Kadel Kurban yana aikin tsaron jama'a daga zuriya zuwa zuriya, a karkashen tasirin da babbansa ke kawo masa, Kadel Kurban yana mayar da hankali sosai kan aikinsa, a sakamakon haka kullum ba ya iya raka iyalinsa, har ma ya kan ji kamar ya yi laifi ga iyalinsa.

A shekarar 2005, mamar Kadel Kurban ta ji rauni, har ma kashin hannunta ya karye, a lokacin, Kadel Kurban yana shan aiki kan wata shari'a, babansa da ke aiki a hukumar tsaron jama'a ta jihar Xinjiang kuma ya yi aiki a wajen. Saboda haka babu wanda ke iya kula da mamarsa. Kadel Kurban ya ce, a wadancan watanni hudu yana jin rashin gaskiya sosai kan mamarsa, amma bai iya yi kome ba, sai nuna gaisuwa ta hanyar buga waya ga mamarsa.

Tun bayan da aka haifi 'dansa, Kadel Kurban ya ajiye shi a gidan iyayensa. A lokacin da 'dansa ke buga masa waya, ya kan tambaye babansa cewa, "Baba, yaushe ne za ka dawo mini gida?" Kadel Kurban ya gaya wa wakilinmu cewa, yana jin nauyi ga 'dansa.

A ganin Kadel Kurban, samun fahinta daga mamarsa da matarsa, da kuma goyon baya daga babansa, suna kara masa kwarin gwiwa ga aikinsa, saboda haka, sai dai ya samu sakamako mai kyau wajen aikinsa kawai, zai iya saka musu alheri.

Sau da yawa an yabawa Kadel Kurban, saboda nasarorin da ya samu kan aikinsa. Yanzu, yana aiki a hukumar kula da ayyukan da suka danganci wasiku da ziyarce ziyarce daga jama'a. Kadel Kurban ya ce, "Aikin kula da wasiku da ziyarce ziyarce daga jama'a, shi ne gadar da ke hada jam'iyya da gwamanti da kuma jama'a, wannan ne kuma babban aiki don kiyaye zaman karko na zamatakewar al'umma, da ba da hidima ga wasannin Olympic, saboda haka, tilas ne na kara yin kokari kan aikina."

Yanzu, Kadel Kurban yana motsa jiki a ko wace rana da safe, ya ce, wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008, shi ne wani gagarumin wasannin da ke jawo hankulan dukkan duniya, a matsayinsa na wani 'dan takarar zama mutumin da ke mika wutar yola, zai yi kokari kan aikinsa, domin sanya jama'ar kabilu daban daban na jihar Xinjiang da su kece raini a wasannin Olympic.