Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-17 16:47:26    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

Asalam alaikum jama'a masu sauraro, barkanmu da wr haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan sabon shiri na labaru masu ban sha'awa na kasar Sin wanda mu kan gabatar da shi a ko wane lahadi domin shere ku.Muna fatan za ku ji dadin shirin. Sai ku kutso akwatin rediyonku ku saurara.

Wani nakasashe yana jin dadin bayar da taimako. An sami wani mutum mai suna Wang Qing a birnin Chongqing da ya bayar da taimakon kudi sama da sau sittin a cikin shekaru hudu da suka shige. Mr Wang Qing shi kurma ne sakamakon wani ciwo mai tsanani da yake fama da shi a yayin da shekaru hudu da haihuwa.A wannan shekara yana da shekaru 44 da haihuwa,har yanzu bai yi aure ba tukuna. A shekara ta 2004 ya kafa wani ofishin ba da taimako ga nakasassu. Kuma shi mai da jagora a gidan sinima. Kowane wata ya kan sami kudin alwas na kudin Sin Yuan dari takwas, da ya ke kudin nan ba shi da yawa, amma ya ba da yawancinsa ga daliban dake fama da talauci a jami'a da sauran mutane. Ya ce "da ya ke ina fama da talauci, ina jin dadin ba da taimako ga saura."

Wani saurayi ya nemi uwarsa. Song Yongjie, wani saurayi ne da ya ke da shekaru 25 da haihuwa a lardin Shandong da ke gabacin kasar Sin yana so ya samo uwarsa kafin ya yi aure. Ya gaya wa wata jaridar wuri ta Chongqing cewa "ni da masoyiyata muna cikin shirin yin aure a wata mai zuwa, abu daya da na ke so in yi shi yanzu shi ne samo uwata ina so in samu fatan alheri daga wajenta,ina so ku ba ni taimako."Masu aikata laifuka sun sayar da uwar Song ne ga wani manomi a lardin Shandong shekara daya bayan ta haifi danta Song. Daga baya 'yan sanda sun kubutar da ita da dawo da ita a wurin mahaifa,duk da haka har yanzu ba ta ga danta ba.

Ana tababar wani mutum. An sami wani tsoho a birnin Lanzhou,babban birnin lardin Gansu dake yammacin kasar Sin wanda ya ke da wani agwagwa mai launin tsanwa a ka, mutanen wuri suna mamaki da ganin haka. A ranar talata da ta shige, yayin da tsohon nan mai suna Wen yana tafiya da agwagwarsa mai ban mamaki a gaban kogin rawaya,wasu mutane sun ga agwagwa da wannan tsoho yana tafiyar da shi,suna tsammanin wannan agwagwa yana cikin tsuntsaye masu daraja da gwamnatin ta ba da kariya sai sun sanar da ofishin 'yan sanda, da 'yan sanda sun isa wurin, sun tambayi tsohon, tsohon ya ce yana kiwon agwagwan,daga baya 'yan sanda sun bincika sun tambayi makwabcinsa wanda ya ba da tabbaci cewa tsohon yana kiwon agwagwa.

An kaddamar da shirin kiyaye muhalli. Gwamnatin lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin ta kebe kudin Sin da ya kai dalar Amurka miliyan 980 wajen kiyaye muhalli a cikin shekaru uku masu zuwa. Bisa shirin da aka tsara an tanadi manyan ayyuka guda goma da suka shafi ayyukan kare gandun daji da wurare masu kayayyakin tarihi da kuma wurare masu damshi, ana sa ran cewa za a kammala ayyuka a shekara ta 2010. An ce a bangren yamma na arewancin lardin da akwai abubuwa masu yawa da ba a taba gani a sauran wuraren kasar Sin ba da kuma dabobbi da tsire tsire masu ban mamaki sosai.gwamnan lardin nan Qin Guangrong ya ce mun dau alkawarin kiyaye muhallin da muke zama a ciki ga kasa mahaifa da duniya gaba daya.

Jama'a masu sauraro,wannan ya kawo karshen shirinmu na yau na labaru masu ban sha'awa na kasar Sin.Mun gode muku saboda kun saurarenmu.(Ali)