Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-17 16:08:40    
Hukumomin shirin sabon kawancen raya Afirka sun shiga cikin kawancen kasashen Afirka, amma babu tabbas ne da zai taimaka domin cimma burinsa

cri

A ran 15 ga wata, shugabannin kasashen Afirka sun shirya wani taro a birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal, inda suka yanke shawarar shigar da hukumomin shirin sabon kawancen raya Afirka wato shirin NEPAD cikin kawancen kasashen Afirka wato AU, domin kawar da hukumominsu da ke da guraban ayyuka daya, da fatan inganta kwarewar hukumomin shirin, domin aiwatar da wannan shiri da kyau da aka tsara wa duk Afirka. Za a gabatar da wannan kuduri ga taron shugabanni na kungiyar AU da za a shirya a watan Yuli a kasar Masar domin zai dudduba shi. Wasu jami'ai masu nazarin lamuran yau da kullum suna ganin cewa, gaskiya ne ya kasance da matsala wajen gudanar da shirin yadda ya kamata, sabo da haka ne, ya zama tilas ne a yi gyare gyare kan hukumomin shirin NEPAD, amma ko zai iya kyautata halin da ake ciki yanzu bayan da ya shiga cikin kungiyar AU ko a'a, ba a iya tabbatar da shi a halin yanzu ba.

Wani abin da ke hana ruwa gudu wajen gudanar da shirin NEPAD yadda ya kamata shi ne, fiye da kimma ne, aka dogara ga taimako daga kasashen yamma. Ya bukaci da makudan kudade da ake aiwatar da shirin NEPAD, ko da yake kasashen yamma masu sukuni su kan yi alkawarin ba da taimako ga kasashen Afirka, amma ba safai su kan cika alkawarinsu ba. Sabo da haka ne, an dakatar da gudanar da ayyuka da yawa, ko an cire su da yawa. Shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade, wanda ya zama daya daga mutanen da suka kaddamar da shirin NEPAD, ya taba kokawa da cewa, hukumomin shirin sun zama wuraren da ake magana kawai, amma ba a gudanar da shi ba.

Sabo da haka ne, muna iya ganin cewa, mai yiyuwa ne, shigar hukumomin shirin NEPAD cikin kungiyar AU zai taimaka wajen yin mu'amala da samun sulhuntawa a tsakanin hukumominsa daban daban, da kuma saukaka ajandar ayyukansu, da kuma karfafa ingancin ayyukansu, amma ba zai zama wata muhimmiyar hanya da ake bi domin daidaita matsalolin da ake fuskanta a hakika ba. Da farko dai, kasashen Afirka sun bukaci wani yanayin zaman al'umma na zaman lafiya da zaman karko, a sa'i daya kuma, su kara karfafa kwarewarsu na samun bunkasuwa cikin gashin kansu, da kuma su yi amfani da fifiko da suke da shi kan makamashi, su hada kansu, da kuma kago sharadi da kokarin da suke yi cikin hadin gwiwa, domin cimma burin samun bunkasuwa tare.(Danladi)