 A ran 16 ga wata, da misalin karfe 11 na yamma, agogon wurin, wutar wasannin Olympic na Beijing ta tashi daga birnin Islamabad, hedkwatar kasar Pakistan, kuma zuwa birnin New Delhi, hedkwatar kasar India, inda za a ci gaba da mika wutar.
Ran nan, da misalin karfe 5, a gogon wurin, an kunna wutar yola ta gasar wasannin Olympic na Beijing a filin wasa na Jinnah a birnin Islamabd, kuma an fara mika ta. Akwai masu mika wutar yola guda 65 sun shiga aikace-aikacen nan da ya shafe awa daya da mintoci 30 ana yinsu. Shugaban kasar Pakistan Mr. Pervez Musharraf, da firaministan kasar Mr. Yusaf Raza Gilani, da shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasar Mr. Arif Hasan, da jakadan kasar Sin dake kasar Pakistan Mr. Luo Zhaohui, da dai sauransu sun halarci bikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics.
Birnin Islamabad ta zama zango na 9 na wannan gagarumin bikin yawo da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing a ketare, kuma wannan ya zama karo na farko ne da wutar wasannin Olympic ta kai birnin nan. (Zubairu)
|