An tsai da cewa, a ran 17 ga wata da yamma, za a yi bikin mika wutar wasannin Olimpic na Beijing a birnin New Delhi, hedkwatar kasar Indiya, wanda ya zama zango na 11 ke nan da ake yin bikin mika wuta. A ran 16 ga wata da magariba, kwamitin wasannin Olimpic na Indiya ya kaddamar da tsarin mikar wutar a birnin New Delhi, mutanen da za su dauki nauyin mika wutar sun nuna kyakkyawar maraba ga wutar wasannin Olimpic na Beijing, kuma suna zura ido a kan wasannin Olimpic na Beijing. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku cikakken bayanin da wakiliyarmu ta ruwaito mana daga Indiya.
A gun taron manema labaru da aka shirya, Mr. Sureh Kalmadi, shugaban kwamitin Olimpic na Indiya yana cike da imani kan matsalar kwanciyar hankali da ta jawo hankulan mutane ya nanata cewa, gwamnatin da kwamitin wasannin Olimpic na Indiya za su dauki dukkan matakan domin tabbatar da kwanciyar hankali ga bikin mika wutar wasannin Olimpic da za a yi a birnin New Delhi. Ya bayyana cewa, "Mun riga mun dauki matakai mafiya kyau domin samun kwanciyar hankali, matakan da muka dauka ba su gaza wa na sauran birane ba ko kusa. Ba mu son ganin mummunan halin da ya faru a London da na Paris, mika wutar wasannin Olimpic lami lafiya ya zama hakki ne ga kasarmu wato Indiya".
Kafin wannan kuma Mr. Zhang Yan, jakadan kasar Sin da ke Indiya ya riga ya nuna godiya ga bangaren Indiya bisa tsarin da ya shirya da alkawarin da ya dauka domin samun kwanciyar hankali, musamman ma ya ji dadi sosai ga hanyar da aka zaba wajen mika wutar, ya ce, "Ana iya cewa, wurin da za a shirya bikin mikar wutar wata muhimmiyar shiyya ce ta duk kasar Indiya baki daya, kuma shiyya ce mafi kayatarwa ta birnin New Delhi, shiyyar nan tana da halin wakilci wajen nuna halayen kasar Indiya. A nan ne akan shirya manyan bukukuwan kasar Indiya, ciki har da murnar ranar bikin kasa."
Bisa sabbin sunayen da kwamitin wasannin Olimpic na Indiya ya bayar an ce, da akwai mutane 70 wadanda za su shiga aikin mika wutar a birnin New Delhi, daga cikinsu kuma da akwai 'yan wasannin motsa jiki 47. Mr. Leander Paes, tamkar wani tauraro ne mai haske na wasan tennis na Indiya wanda zai halarci wasannin Olimpic a kawo na 5 ya ce, tun lokacin da yake yaro ya yi mafarkin shiga wasannin Olimpic, kome dalilin siyasa ba zai iya hana shi shiga wasannin Olimpic ba, kuma ba zai iya hana shi shiga aikin mika wutar wasannin Olimpic ba. Ya bayyana cewa, "Ina maraba da zuwan wutar wasannin Olimpic a kasar mahaifata wato Indiya. Bisa matsayina na daya daga cikin masu mika wutar, ina jin alfahari sosai. Bisa matsayinmu na 'yan wasannin motsa jiki, dole ne mu dauki hakkin da ya rataya a wuyanmu yadda ya kamata, kuma dole ne mu nuna adawa ga tunanin sanya siyasa cikin wasannin motsa jiki."
Mr. Wang Hongsen, wakilin bangaren Sin wajen mika wutar, kuma manajan direktan kamfanin Indiya na rukunin narke karafan kasar Sin ya yi alfahari sosai sabo da ya yi sa'a da ya zama wakilin Sinawa wajen mikar wutar wasannin Olimpic a kasar Indiya, ya ce, "Bayan da na samu labarin da zan zama mai mikar wutar, ina ta kara motsa jikina, amma ba ni kadai ba, dukkan ma'aikatan kamfannin su ma sun yi haka". (Umaru)
|