Wani nas, dan kabilar Tibet da ya taba samu lambar Nightingale na farko Pasang Dhondup ya furta cewa, ko kabilar Tibet da kabilar Han dukkansu Sinawa ne.
A ran 16 ga wata a cikin asibitin jama'a na yankin Ganzi mai cin gashin kansa na lardin Gansu, a yayin da Pasang Dhondup yake magana kan batun tashe-tashen hankula ya yi mamaki cewa, kasar Sin ta samu bunkasuwa sosai, jama'a suna kara jin dadin zama, don me wasu tsirarrun mutane suka nemi raba kasar mahaifa? Addinin Budda ya yi kira da a ji tausayi da ba da gudummowa, amma wasu mutane sun tada tarzoma, su ba hakikanan masu bin aninin Budda ba.
Pasang Dhondup ya nuna cewa, kabilar Tibet ko kabilar Han, kabilu 56 dukansu 'ya'yan kasar mahaifa ne, dukansu membobin iyalan kabilar Sin ne, muna da jini irin bai daya, ba wanda ke iya raba mu.(Lami)
|