Madam Bi Hua, mataimakin babban direktan cibiyar nazarin ilmin Tibet ta kasar Sin, kuma shugaban nazarin zamanin yanzu ta bayar da wani bayani a jaridar Guangming Daily ta kasar Sin da aka wallafa a ran 16 ga wata, inda ta nuna cewa, Dalai Lama da rukuninsa suna da alhakin da za su iya kaucewa ba kan lamarin nuna karfin tuwo da aka yi a ran 14 ga watan Maris a birnin Lhasa na jihar Tibet mai cin gashin kanta.
A cikin bayaninta, madam Bi ta ce, a kwanan baya, lokacin da aka ta da lamarin nuna karfin tuwo a birnin Lhasa na jihar Tibet da sauran yankunan da 'yan kabilar Tibet suke da zama, kuma a lokacin da aka hallaka rayukan fararen hula da ba su ji ba su gani ba, kuma a lokacin da tsirarrun masu bin addinin Buddha da suka aikata laifin ta'addanci, ba ma kawai Dalai Lama bai nuna tausayinsa kamar yadda kowane mai bin addinin Buddha yake yi ba, hatta ma ya saba da babbar ka'idar addin Buddha, ya yi karya kuma ya ci gaba da yaudaran jama'a da tsirar da kansa daga alhakan da ya kamata ya dauka. Wadannan abubuwan da Dalai Lama na zuriya ta 14 ya yi sun bata ran Bi Hua baki daya.
Wannan bayani ya nuna cewa, tun lokacin da Dalai Lama da rukuninsa suka gudu, su kan yada tunaninsu na nuna adawa da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da sabuwar kasar Sin a kullum, kuma su kan yi yunkurin kebe yankin Tibet daga kasar Sin domin farfado da ikon mulkinsu a yankin Tibet. Sabo da haka, su kan yada jita-jita domin lalata kasar Sin, har ma suna yunkurin yin amfani da rayukan sauran mutane domin cimma burinsu. (Sanusi Chen)
|