Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-16 17:44:53    
Batun Tibet yana da nasaba da ikon mulkin kasar Sin da cikakkun yankunanta

cri
A ran 16 ga wata, jaridar People's Daily ta kasar Sin ta bayar da wani bayani mai lakabi haka, "Mene ne asalin batun Tibet?" A cikin wannan bayani, an nuna cewa, a hakika dai, batun Tibet ba batun hakkin dan Adam ba, kuma ba batu na addini ba, haka nan kuma ba batu ne na kabilanci ba, shi batu ne da ke da nasaba da ikon mulkin kasar Sin da cikakkun yankunanta, wato yana da nabasa da babbar moriyar al'ummar Sinawa.

A cikin wannan bayani, an zargi maganar da rukunin Dali ya yi, wato ya ce, batun Tibet, batutuwa ne na dan Adam da addini da na Kabila. Wannan bayani ya nuna cewa, har zuwa farkon rabin karni na 20 da ya gabata, yankin Tibet yana cikin tsarin mulkin kama karya da yake hada harkokin siyasa da addini tare. Wannan tsari ya fi tsarin da aka bi lokacin da kasashen Turai suke matsayin wayin kai na lokacin tsaka tsakiya muni. Amma yanzu, ana shimfida tsarin kiwon lafiya da ba da ilmin tilas da ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta a duk fadin jihar Tibet. A waje daya kuma, jama'ar Tibet suna da cikakken ikon wajen bin addininsu. Ana kuma cetowa da kiyaye al'adun Tibet.

Bugu da kari kuma, wannan bayani ya ce, "batun Tibet" ya kasance tamkar kayan aiki da rukunin Dalai yake amfani domin yunkurin neman 'yanci kan Tibet. A hakika dai, batun Tibet batu ne da ke da nasaba da ikon mulkin kasar Sin da tabbatar da cikakkun yankunanta. Dukkan yunkurin lalata ikon mulkin kasar Sin da sa hannu a cikin harkokin gida na kasar da sunan "batun Tibet " da kowane dalilai daban yunkurin banza ne. (Sanusi Chen)