Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-16 16:30:43    
Kasar Sin na son ciyar da dangantakar da ke tsakaninta da Japan ta samun moriyar juna bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni gaba

cri
Yau 16 ga wata, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin, kuma shugaban kasar Hu Jintao ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin na son yin kokari tare da kasar Japan, don kara yin cudanya da hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban daban, da sa kaimi ga dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta samun moriyar juna bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, da kuma tabbatar babban makasudinsu na yin zaman tare cikin lumana, da hadin gwiwa na samun moriyar juna, da kuma samun bunkasuwa tare.

Mr. Hu Jintao ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake ganawa da kungiyar wakilai ta jam'iyyun da ke kan karagar mulki ta kasar Japan, wadda ke karkashin shugabancin Mr. Ibuki Bun mei, babban daraktan jam'iyyar 'yancin kai da dimokuradiya, da Mr. Kitagawa Kazuo, babban daraktan jam'iyyar Komei. Inda ya yi jinjina sosai ga dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Japan, da kuma cudanyar da jam'iyyun kasashen biyu suke yi a yanzu. Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, jam'iyyar kwaminis da gwamnatin kasar Sin na mayar da hankali sosai kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Japan, kuma yalwata dangantaka mai darewa ta zaman jituwa da makwabtaka a tsakanin kasashen biyu, wannan shi ne manufar da kasar Sin ke tsayawa a kai.

Mr. Ibuki Bun Mei, da Mr. Kitagawa Kazuo sun bayyana cewa, jam'iyyun da ke kan karagar mulki na kasar Japan, da jama'ar kasar za su yi kokari don ciyar da dangantakar samun moriyar juna bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu gaba, da kara kawo alheri ga jama'ar kasashen biyu, da kuma kara kiyaye zaman karko da bunkasuwar Asiya, har na dukkan duniya.

A ranar 15 ga wata ne, kungiyar wakilai ta jam'iyyun da ke kan karagar mulki na kasar Japan ta iso nan birnin Beijing, don fara ziyararta ta kwanaki biyu a nan kasar Sin. A wannan rana kuma, Mr. Dai Bingguo, wakilin majalisar gudanarwa ta kasa Sin, da kuma Mr. Wang Jiarui, ministan kula da harkokin cudanya da ketare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sun gana da kungiyar wakilan daya bayan daya. (Bilkisu)