Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-16 15:39:45    
Kasar Amurka za ta shirya 'yan wasa kusan 600 wajen shiga gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri
Shugaban kwamitin kula da wasannin Olympics na kasar Amurka Mr. Uberroth ya yi bayani a ran 15 ga wata a birnin Chicago na kasar, cewa kwamitin zai shirya 'yan wasa kusan 600 wajen shiga gasar wasannin Olympics da za a yi a birnin Beijing a watan Agusta na shekarar nan.

Mr. Uberroth ya fadi haka ne a ran nan lokacin da yake halartar taron koli na watsa labarai na kungiyar 'yan wasannin Olympics ta kasar Amurka. Kuma ya kara da cewa, tawagar Amurka ba za ta nuna adawa da gasar wasannin Olympics ta Beijing ba, kuma ba a bukatar sake jaddadawa a kan batun. Har ma Mr. Uberroth ya ba da shawara ga wadanda suka yi furucin cewa, wai ba za su halarci bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing ba, cewa ina fatan za su iya bayar da tikitin halarci bikin ga 'yan iyali na 'yan wasa na kasashe daban daban.(Kande Gao)