Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-16 14:07:14    
Kadaici ya iya yin illa sosai ga lafiyar jiki

cri

Bisa wani sakamakon nazarin kimiyya da manazarta na kasar Amurka suka bayar a kwanan nan, an ce, ba kawai mutanen da ya kan ji kadaici cikin dogon lokaci su kan nuna barin rai ga zaman rayuwa ba, har ma jikinsu zai samu rashin lafiya.

Kwararru a fannin ilmin tunanin dan Adam na jami'ar Chicago ta kasar Amurka sun bayyana cewa, domin tabbatar da dangantakar da ke tsakanin kadaici da lafiyar jiki, sun fara gudanar da wani bincike ga mutanen da shekarunsu ya kai kimanin 20 da haihuwa yau da shekaru gomai da suka gabata, har zuwa shekarunsu ya kai 50 zuwa 68 da haihuwa. A cikin wadannan mutane, wasu mutane sun suna fama da kadaici, ba su yin cudanya da sauran mutane, wasu kuwa suna son yin mu'amala da sauran mutane, kuma su kan shiga harkokin zaman al'umma iri daban daban.

Sakamakon binciken ya bayyana cewa, ko da masu kadaici, ko da masu son yin cudanya da sauran mutane, sun taba gamuwa da dimbin matsaloli a fannonin neman samun ilmi da neman samun guraban aikin yi da neman soyayya da kuma horar da yaransu. Amma sun sha bamban sosai lokacin da suke warware matsalolin.

Game da masu kadaici, bakin ciki da suka ji lokacin da suke girma ya kan yi illa ga ra'ayinsu na zaman rayuwa. Kuma lokacin da suke shiga mawuyacin hali, kullum ba su san yadda za su yi ba, har ma ba su son neman taimako daga sauran mutane. Amma masu son yin cudanya da sauran mutane suna iya sa rai kan bakin cikin da suka gamu a cikin zaman rayuwa, suna iya warware matsaloli cikin yakini yadda ya kamata, haka kuma suna son neman taimako daga sauran mutane.

Bugu da kari kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, sabo da masu kadaici ba su iya daidaita abubuwan bakin ciki da suka ji a rai kamar yadda ya kamata ba, shi ya sa kullum karfin bugun jininsu ya fi sauran mutane yawa, ta haka sun fi saukin samun tsofa.

Bisa bayanin da masu ilmin kimiyya na kasar Danmark suka bayar, an ce, hadarin kamuwa da ciwon zuciya da masu zaman kadanci suke yi zai yi ninki daya idan an kwatanta shi da na masu zama tare da sauran mutane.

Manazarta sun bayar da wannan sakamako ne bayan da suka yi bincike kan mazauna dubu 138 da shekarunsu ya kai 30 zuwa 69 da haihuwa da ke shiyyar Arhus ta kasar Danmark. Kuma binciken yana ganin cewa, masu zaman kadanci da shekarunsu ya yi yawa sun fi saukin kamuwa da ciwon zuciya.

Haka kuma bisa labarin da muka samu, an ce, a cikin mutanen da aka yi musu binciken, mutane 646 sun kamu da ciwon zuciya mai tsanani. Kuma maza da shekarunsu ya zarce 50 da haihuwa da mata da shekarunsu ya wuce 60 da haihuwa wadanda suka yi zaman kadanci sun fi saukin kamuwa da ciwon. Ko da yake yawansu ya kai kashi 8 cikin dari na dukkan mutanen da aka yi musu binciken, amma a cikin mutanen da suka mutu sakamakon ciwon zuciya bayan wata guda, mutanen da yawansu ya kai kashi 96 cikin dari su mutane ne da ke yin zaman kadaici.

Ko da ya ke har yanzu manazarta ba su san ina dalilin da ya sa masu zaman kadanci suka fi saukin kamuwa da ciwon zuciya ba, amma suna ganin cewa, shan taba, da yin abubuwa marasa kyau ga lafiyar jiki, da ba safai su kan yi binciken lafiyar jikinsu ba, da kuma rashin kulawa da gayon baya daga iyalansu su ne muhimman dalilan haifar da ciwon zuciya. Ban da wannan kuma sabo da masu zaman kadaici ba su son karbar taimakon da aka bayar gare su, shi ya sa a cikin zaman yau da kullum, abubuwan da su kan yi ba su yi kamar yadda ya kamata ba.(Kande Gao)