Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-16 14:05:41    
Yanayin sararin samaniya na kasar Sin

cri

Bukukuwan yanayin sararin samaniya na kasar Sin suna da tarihin da yawan shekarunsu ya kai dubu biyu ko fiye, su ne abubuwan tarihi na al'adu da jama'ar kasar Sin suka samu bayan da suka dudduba da nazari da kuma takaita abubuwa kan yanayin sararin samaniya cikin 'yanci kuma cikin dogon lokaci. Suna iya bayyana sauye-sauyen yanayin sararin samaniya da ruwan sama da sauran sauye-sauyen da aka samu bisa yanayin sararin samaniya da kuma ba da jagoranci ga ayyukan noma, sun ba da tasiri sosai ga abinci da sutura da tafiye-tafiye na duban iyalai. A takaice dai, an kasa shekara daya cikin matakan lokaci 24 bisa yanayin sararin samaniya, a kowane matakin, alamar yanayin sararin samaniya ta zauna cikin zaman karko, kuma an dora matakin da wani suna. Bikin Qingming ya kan zo a ranar 4 ko biyar ko shida na watan Afril. Bikin Qingming na shekarar da muke ciki zai zo ne a ranar 4 ga watan Afril .

Game da asalin samun sunan Qingming, an bayyana a cikin tsofaffin littattafai na zamani aru-aru cewa, dukkan tsire-tsiren halittu suna tsiro da girma, kuma an sami tsabta da haske sosai a lokacin bikin Qingming , shi ya sa ana cewa, ya kasance da tsabta da haske ke nan a ranar bikin qingming. In ranar bikin Qingming ta zo, sai ake kara ruwan sama da yawa , lokacin ya yi daidai lokaci mai kyau na yin shuke-shuke da sauran aikin noma, saboda haka, akwai karin magana na manoma cewa, kafin ranar bikin Qingming da bayanta, ana soma shuke-shuken wake da ganyayen lambuna da dai sauransu tare kuma dasa bishiyoyi, kada a bata lokacin bikin Qingming. Kai, a gaskiya dai bikin yana da danganta da aikin noma sosai da sosai.


1 2 3