Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-16 13:55:57    
Jama'ar kasar Japan sun yi maraba da ziyara da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao zai kai wa kasarsu

cri
A ran 15 ga wata da dare, tawagar jam'iyyun dake kan karagar mulkin kasar Japan ta bayyana a birnin Beijing cewa, jam'iyyun dake kan karagar mulkin kasar Japan da jama'ar kasar sun yi maraba da ziyara da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao zai kai wa kasarsu, suna fatan za a iya cimma nasarar ziyarar nan kuma a samu sakamako mai kyau.

Tawagar jam'iyyun dake kan karagar mulkin kasar Japan dake karkashin jagorancin babban direktan jam'iyyar LDP da takwaran aikinsa na jam'iyyar JKP ta iso birnin Beijing ne a ran 15 ga wata, kuma ta fara ziyarar aikin kwanakin biyu a kasar Sin. Lokacin da suka gana da wakilin majalisar gudanarwa ta kasa Sin Mr. Dai Bingguo, sun bayyana cewa, jam'iyyun dake kan karagar mulkin kasar Japan tana son ta yi kokarin shara fage ga ziyarar da Mr. Hu Jintao zai kai wa kasar Japan.

Mr. Dai Bingguo ya ce, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao zai kai wa kasar Japan ziyara a cikin 'yan kwanakin gaba, kuma wannan yana da muhimmanci sosai ga kasashen biyu kan karfafa amincewar juna a siyasa, da tsara shirin raya dangantaka dake tsakanin kasashen biyu cikin dogon lokaci.

Ran nan kuwa, Ministan kula da harkokin cudanya da kasashen ketare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Wang Jiarui shi ma ya gana da tawagar jam'iyyun dake kan karagar mulkin kasar Japan a birnin nan Beijing. Ya bayyana cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana son ta yi kokari tare da jam'iyyun dake kan karagar mulkin kasar Japan, don karfafa kyakkywar hali da bunkasuwar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu, da kuma sa kaimi ga an samu nasarar ziyarar shugaba Hu Jintao a kasar Japan. (Zubairu)