Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-16 13:07:27    
Wasu kafofin watsa labaru na kasashen ketare sun yi tunani kan aikace-aikacen rashin basira da 'yan kasashen yamma kadan suka yi kan aikin mika wutar yola ta wasannin Olympics

cri

Yanzu, an wuce rabin yunkurin mika wutar yola ta wasannin Olympics ta Beijing a kasashen ketare. Kwanan baya, wasu kafofin watsa labaru na kasashen ketare sun soma yin tunani kan aikace-aikacen rashin basira da jama'a da shugabannin wasu kasashen yammaci kadan suka yi kan aikin mika wutar yola ta wasannin Olympics.

Jaridar Gulf News, wato jaridar da ake bugawa da Turanci, wadda ta fi girma a yankin Gulf, ta yi bayyani a ranar 14 ga wata cewa, an ga alamar cewa, birnin Beijing ya shirya wasannin Olympics, wannan ya ba da dama ga wasu shugabannin kasashen yamma wajen nuna ma'auninsu na jin kai, da manufar hakkin bil Adam, da kuma ra'ayin girman kai. Amma, wannan ba ya da ma'ana ko kadan, zai kawo cikas ga wannan gaggarumin wasannin motsa jiki da ake shiryawa sau daya a ko wadanne shekaru hudu, wanda jama'a da 'yan wasannin motsa jiki na kasashe daban daban suke sa ido a kai.

A ranar 15 ga wata, jaridar The Wall Street Journal ta bayar da labari game da ziyarar da ta yi ga madam Susan brownell, wata masaniya daga kasar Amurka da ke yin ziyara a nan kasar Sin. Tana ganin cewa, ba kawai kasar Sin za ta iya shirya wani wasannin Olympics cikin nasara ba, har ma za ta zama wata kasar shirya wasannin Olympics da ake girmamawa. Tana ganin cewa, ko da ya ke ana kasancewa da wasu matsaloli a kasar Sin, amma wasu mutanen kasashen yamma sun yi fatali da cigaban da kasar Sin ta samu a 'yan shekarun da suka wuce. (Bilkisu)