A ran 15 ga wata, Liu Qi, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing ya mika wasika ga kungiyar gudanar da aikin mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing domin gabatar da sabbin bukatu da buri gare ta.
A cikin wasikar, Mr. Liu Qi ya yi fatan za a iya hadin gwiwa da kuma daina tsoratarwa da kawo wahaloli domin neman samun nasara a cikin wannan aiki.
Haka kuma a cikin wasikar, Mr. Liu ya ce, daga ran 1 ga wata, kungiyar gudanar da aikin mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing tana ta fuskantar hali mai sarkakiya da ake ciki a ketare, amma 'yan kungiyar sun hada gwiwarsu sosai wajen kau da munanan abubuwan da suka kawo cikas ga aikin, ta haka sun kiyaye kwarjinin kasar Sin da kuma na wutar gasar wasannin Olympics, da rinka samun nasara a cikin wannan aiki, da kuma samun girmamawa daga jama'ar duk duniya.(Kande Gao)
|