Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-15 20:23:09    
Bangaren Sin ya yi imanin cewa, kasar Indiya za ta samar da taimako kan mika wutar gasar wasannin Olympics a kasar

cri
A ran 15 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Jiang Yu ta yi bayani a birnin Beijing, cewa bangaren Sin ya yi imanin cewa, aikin mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing da za a yi a kasar Indiya zai samu goyon baya da taimako daga dukkan 'yan kasar da kuma gwamnatin kasar.

Kuma Madam Jiang ta bayyana cewa, bangaren Sin ya yi imanin cewa, kasar Indiya za ta dauki tsauraran matakai wajen kare aikin mika wutar gasar wasannin Olympics a kasar lami lafiya. In za a samu kungiyar neman 'yancin kan Tibet da za ta lalata aikin a kasar Indiya, to ba yadda za a yi sai za a iya sake gano ainihinta na neman kawo wa kasar Sin baraka.(Kande Gao)