Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-15 20:22:23    
Kasar Thailand tana adawa da a hada batun Tibet da gasar wasannin Olympics tare

cri
A ran 15 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Thailand Noppadon Patama ya yi bayani a birnin Beijing, cewa batun Tibet batun cikin gida ne na kasar Sin, kasar Thailand tana adawa da a hada batun da gasar wasannin Olympics tare.

Mr. Noppadon ya fadi haka ne lokacin da yake yin shawarwari tare da ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi. Kuma ya ce, bangaren Thailand zai tsaya tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya. Kuma ya yi imanin cewa, kasar Sin za ta shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin nasara, wadda dukkan jama'ar kasashen Asiya za su ji alfahari da ita.(Kande Gao)