Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-15 20:12:47    
An yi maraba da wutar wasannin Olympic ta Beijing da hannu biyu biyu daga dukkan fannoni a Muscat

cri

Saurari

A ran 14 ga wata, lokacin da aka isar da wutar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Muscat, wannan birni ya zama birnin da ke cike da farin ciki.

Jiragen sama masu saukar ungulu suna zagaya a sararin sama, kananan jirgin ruwa suna iyo a cikin teku. A waje daya kuma, gidan rediyo na Oman yana watsa da shirye-shirye na sa'o'i 4 kai tsaye game da aikin mika wutar. Da karfe 5 na yamma na ran 14 ga wata, an soma aikin mika wutar wasannin Olympic ta Beijing a filin Bustan na birnin Muscat, babban birnin kasar Oman. Mr. Liu Jinming, mataimakin shugaba mai zartaswa na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya nuna wa jama'ar Oman wutar.

A gun bikin maraba da isar wutar wasannin Olympic ta Beijing a kasar Oman, malam Ali Bin Masoud, ministan wasannin motsa jiki na kasar Oman kuma shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasar Oman ya ce, "Da hannu biyu biyu ne, muke maraba da zuwan wutar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008 da kungiyar wakilan kasar Sin. Ko da yake wutar wasannin Olympic ta Beijing zai dan tsaya kawai a Muscat, amma wannan wuta za ta ci gaba da hura a cikin zuciyata da zuciyoyin dukkan mutanen da suke halartar wasannin motsa jiki ta Olympic."

An aiwatar da aikin mika wutar wasannin Olympic ta Olympic ta Beijing daga filin Bustan. A cikin masu rike da wutar yola, wani dalibi mai suna HassanSuker wanda ke karatu a wata makarantar midil ya jawo hankulan mutane sosai. Bayan da aka soma aikin, ya bi sawun sauran masu rike da wutar yola har tsawon kilomita fiye da 10. Lokacin da yake gudu, ya kuma gaya wa wakilinmu cewa, "Ina jin alfahari sosai domin isar wutar wasannin Olympic ta Beijing a kasarmu Oman. Ni dan kasar Oman ne. Na gudu tare da wutar sabo da ina son bayyana cewa, mutanen kasar Oman suna goyon bayan abokan Sinawa. Ina son kasar Sin, ina kuma son kasar Oman. Ina goyon bayan kasar Sin, ina kuma goyon bayan kasar Oman."

Yawan masu rike da wutar yola a birnin Muscat ya kai 80. Galibinsu sun zo kasar Oman da sauran kasashen Larabawa. Ko da yake suke yin aiki iri daban-daban, amma dukkansu suna jin alfahari sosai domin shigarsu a cikin wannan aikin mika wutar wasannin Olympic ta Beijing. Madam Lailah Saeed wadda take mika wutar, wata gurguwa ce. Ko da yake ta kan ji zafi sosai domin ta dade tana shan magani, amma ta gaya wa wakilinmu cewa, "Ina taya murna ga gasar wasannin Olympic ta Beijing ta zangon gidan rediyon kasar Sin. Na gode wa birnin Beijing."

Wasu mutanen birnin Muscat sun sani an taba lalata aikin mika wutar wasannin Olympic ta Beijing a wasu kasashe. Ba su amince da aka yi haka ba. Bayan da malam Abdullah bin Hamad wanda ya kafa tushen raya wasannin Olympic a kasar Oman, kuma shugaban farko na kwamitin wasannin Olympic na kasar ya gama aikin mika wutar, ya gaya wa wakilimu cewa, "Wasu mutane suna son kin halartar gasar wasannin Olympic. Na gaza fahimtar abubuwan da suke yi. Wasu kafofin watsa labaru ma suna yada labaru ba na gaskiya ba. Ba za mu mai da hankulanmu kan irin wadannan labaru ba."

An samu nasara sosai wajen mika wutar wasannin Olympic ta Beijing a kasar Oman. Jama'ar kasar Oman sun bayyana yadda suke maraba da wutar wasannin Olympic ta Beijing, kuma suke goyon bayan gasar wasanin Olympic ta Beijing.