Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-15 18:01:38    
Kasar Sin tana sa kaimi ga aikin hana shan taba bisa damar shirya wasannin Olympics

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri. Sanin kowa, shan taba ya yi illa sosai ga lafiyar jikin dan Adam, mutane kimanin miliyan guda su kan mutu sakamakon cututtukan da ke da nasaba da shan taba a kasar Sin a ko wace shekara. Domin samar da wani kyakkyawan muhallin zaman al'umma da ke iya ba da taimako ga aikin hana shan taba, birnin Beijing ya bayar da wata ka'ida a kwanan nan, inda karo na farko ne aka bukaci daina shan taba a cikin dakunan cin abinci da otel-otel da cibiyoyin horaswa da wuraren shan iska da dai sauran wuraren jama'a, ta haka ta jawo hankalin zaman al'umma sosai. To, a cikin shirinmu na yau, bari mu leka batun."Na kan ji bakin ciki sosai in na ga mijina yana shan taba, amma bana iya hana shi, shi ya sa ba yadda zan yi sai sai na bar wurin."

Masu sauraro, muryar da kuka saurara dazun nan rashin gamsuwa ne da Madam Sun Xiaoya da ke da zama a unguwar Wang Jing ta birnin Beijing ke nuna wa mijinta. Mijinta Li Jianhua ya riga ya sha taba har shekaru fiye da 30, kuma tun tuni shan taba ya riga ya zama wani kashi ne na zamansa na yau da kullum. Madam Sun ta bayyana cewa, da zarar ta janyo hankalin mijinta don ya bar shan taba, sai ya ba da dalilinsa na shan taba. "Na kan sha taba idan na ji farin ciki da bakin ciki, da maraba da baki, da kuma ci abinci tare da sauran mutane."

A kwanan nan, an sanar da wata sabuwar ka'ida game da hana shan taba a wuraren jama'a na birnin Beijing a tashar Internet ta gwamnatin birnin Beijing domin neman ra'ayoyin jama'a. A cikin ka'idar, an kara yawan wararen hana shan taba, kuma karo na farko ne a bukaci masu shan taba su daina shan taba a ciki da kuma wajen dakunan wasanni da na motsa jiki, a waje daya kuma karo na farko ne aka hana shan taba a cikin dakunan cin abinci da otel-otel. Ta haka, ana iya ganin cewa, jami'an kiwon lafiya na birnin Beijing sun mayar da gasar wasannin Olympics ta shekara ta 2008 a matsayin wata kyakkyawar dama wajen sa kaimi ga aikin hana shan taba. Wannan sabuwar ka'ida ta jawo hankulan mazaunan birnin Beijing sosai, dimbinsu sun nuna goyon baya gare ta, kuma suna ganin cewa, hana shan taba zai ba da taimako ga lafiyar jikin dan Adam, haka kuma zai samar da wani kyakkyawan muhallin zaman al'umma ga gasar wasannin Olympics da za a yi ba da jimawa ba. Madam Sun da muka ambata a baya ita ce daya daga cikin masu goyon bayan ka'idar. "Ina goyon bayan ka'idar kwarai da gaske. Ko a wuraren jama'a ko a cikin gida, shan taba zai yi illa ga lafiyar jikin iyalai da abokai, bai kamata ba a sha taba da ke yin illa ga mai shanta da sauran mutane."

Shekarar bana shekara ce ta uku da aka kaddamar da bin yarjejeniyar tsarin hana shan taba ta kungiyar kiwon lafiya ta duniya a kasar Sin. Inganta aikin aiwatar da yarjejeniyar da kuma kafa tsarin hana shan taba wani muhimmin aiki ne da ke gaban kome a cikin ayyukan hana shan taba a kasar Sin. Madam Jiang Yuan, mataimakiyar shugaban ofishin hana shan taba na cibiyar sarrafa cututtuka ta kasar Sin tana ganin cewa, bayan da aka gudanar da sabuwar ka'idar hana shan taba a wuraren jama'a na birnin Beijing, yawan masu shan taba a wuraren jama'a zai ragu, ta haka, yawan masu shan taba na birnin Beijing zai ci gaba da raguwa. Kuma ta kara da cewa, "A ganina, muhallin hana shan taba na yanzu ya fi kyau bisa na shekaru da dama da suka gabata, kuma yawan mutanen da ke da hannu cikin aikin hana shan taba ya karu. Sabo da haka halayyar zaman al'umma za ta samu kyautatuwa." (Kande Gao)