Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-15 15:30:55    
Hadaddiyar gwamnatin kasar Kenya tana fuskantar kalubale da dama

cri

A ran 13 ga wata a birnin Nairobi, shugaban kasar Kenya Mr Mwai Kibaki ya sanar da cewa, Jam'iyyar PNU wato Party of National Unity da yake shugabanta da kuma babbar jam'iyyar adawa ta ODM wato Orange Democratic Movement da Mr Raila Odinga yake shugabanta sun kafa hadaddiyar gwamnati, haka kuma ya nada Mr Odinga da ya zama firayin ministan kasar. Wannan sakamako ya kawo karshen rikicin babban zabe na kasar Kenya, kasar Kenya ta samu wani babban ci gaba na shimfida zaman lafiya. Amma wasu jami'ai masu nazarin lamuran yau da kullum suna ganin cewa, sabuwar hadaddiyar gwamnatin kasar Kenya tana fuskantar kalubale da dama.

A gun wani taron manema labaru da aka shirya a ran 13 ga wata a fadar shugaban kasar, Mr Kibaki ya yi alkawarin cewa, hadaddiyar gwamnati za ta yi duk kokari da take iya yi, domin cimma burin shimfida zaman lafiya da dinkuwar kasa da zaman karko a kasar Kenya, haka kuma ya sa kaimi ga dukkan mambobin majalisar ministoci da su yi kokari a guraban ayyukansu, domin taimakawa kasar Kenya da ta maido da zaman karko tun da wuri.

Babbar jarida da ta fi muhimmanci ta kasar Kenya wato jaridar Daily Nation ta bayar da wani sharhin edita a ran 14ga wata cewa, ko da yake hadaddiyar gwamnati ta kafu, amma tana fuskantar kalubale da dama. Matsala ta farko ita ce, ko jami'an gwamnati suna iya hada kansu bisa gaskiya domin kula da harkokin kasar Kenya da kyau ko a'a. Manyan hukumomin gwamnati suna hannun jam'iyyun biyu, sabo da haka, mai yuyuwa ne, za su kawo cikas ga juna.

Ban da wannan kuma, matsalar tattalin arziki ta zama wani kalubale daban da ke gaban sabuwar gwamnati. Rikicin babban zabe ya lalata tattalin arzikin kasar Kenya sosai. Yawan karuwar tattalin aiki da kasar za ta samu a shekarar bana da aka yi hasashe ya ragu daga kashi 6.9 daga cikin dari zuwa kashi 4.5 daga cikin dari. Farashin kayayyaki na kasar Kenya ya kara hauhawa a sakamakon saurin karuwar farashin hatsi a kasuwar duniya. Sabo da haka ne, jama'ar kasar Kenya ke shan wahala a zaman rayuwarsu.

A halin yanzu, gwamnatin kasar Kenya tana daukar matakai, domin tsugunar da manoma da suka rasa gidajensu a sakamakon rikicin babban zabe, domin su maido da zaman rayuwarsu yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar Kenya ta kaddamar da hukumar raya arewacin yankin kasar Kenya da sauran wuraren da ke fama da fari, domin bunkasa wadannan yankunan da aka kyale su a da, da kuma kara kyautata zaman rayuwar jama'a na wuraren. Hadaddiyar gwamnati tana inganta amincewa daga jama'a ta hanyar daukan wasu matakan jin dadin jama'a, ta yadda za ta iya share fage wajen tafiyar da mulkinsu a nan gaba. Ko manufofin da hadaddiyar gwamnatin kasar Kenya take dauka ko za ta dauka za su yi amfani ko a'a, mene ne canzawar makoma ta halin siyasa a nan gaba ? Bari mu zura ido kan hakan.(Danladi)