Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-15 15:29:54    
Masu bin addinin Budda na garin Abe na kasar Sin sun daga tutar kasa kuma shuka itatuwa don kawo alheri ga gasar wasannin Olympic na Beijing

cri
A ran 14 ga wata, masu bin addinin Budda na wurin ibada mai suna Tsannyi Monastery a garin Abe na jihar Sichuan na kasar Sin sun daga tutar kasar, da kuma shuka itatuwa don kawo alheri na zaman lafiya ga gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Tun daga shekarar 1984, wurin ibada mai suna Tsannyi Monastery ya fara yin aikace-aikace na daga tutar kasa da shuka itatuwa a ko wace shekara, don kiyaye yanayin kasa a mafarin kogin Yangtse. Shekarar nan shekara ce da za a shirya gasar wasannin Olympic a birnin Beijing, itatuwa sama da dubu daya da masu bin addinin Budda suka shuka sun bayana fatan alherinsu na cimma nasarar shirya gasar wasannin Olympic.

Masu bin addinin Budda a warin ibada na Tsannyi Monastery sun bayyana cewa, gasar wasannin Olympic babbar gasa ce na dukkan mutanen duniya, kuma abin farin ciki ne gare mu Sinawa. Dukan mutane masu son zaman lafiya sun yi fushi sabo da laifin da aka yi bisa jagorancin Rukunin Dalai Lama na kawo cikas ga mika wutar wasannin Olympic.

Ran nan kuwa, sauran wuraren ibada masu bin addinin Buddha irin na Tibet a yankin cin gashin kan kabilar Zang da kabilar Qiang a garin Abe na jihar Sichuan kuma sun yi aikace-aikace don kawo alheri ga gasar wasannin Olympic na Beijing. (Zubairu)