Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-15 10:46:49    
Birtaniya ta ki amincewa da a saka batun siyasa a gasar wasannin Olympics, a cewar wakilin musamman na firaministan Birtaniya

cri
Wakilin musamman na firaministan Birtaniya, kuma ministan kudi na kasar Alistair Darling, wanda ke halartar shawarwarin tattalin arziki da kudi a karo na farko tsakanin Sin da Birtaniya ya bayyana jiya 14 ga wata a nan birnin Beijing cewar, yunkurin kauracewa gasar wasannin Olympics ta Beijing babban kuskure ne, bangaren Birtaniya ya ki amincewa da a saka batun siyasa a gasar wasannin Olympics. Ya ce, firaministan Birtaniya Gordon Brown zai halarci bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing, kuma yana fatan za a shirya kasaitacciyar gasar wasannin Olympics a kasar Sin.

Mr. Darling ya fadi haka ne yayin da ya yi wata ganawa da memban majalisar gudanarwa ta kasa Sin Dai Bingguo. Bangarorin biyu sun sami ra'ayi daya cewar, za su kokarta tare, domin kara zurfafa dangantakar dake kasancewa tsakaninsu a fannoni daban-daban.

A nasa bangare kuma, Mr. Dai ya bayyana gaskiyar munanan laifuffuka da aka barkata na tada tarzoma a jihar Tibet kwanan baya, da hakikanin halin da ake ciki, haka kuma ya nanata matsayin da gwamnatin Sin ke tsayawa a kai. Mr. Darling ya yi nuni da cewar, batun Tibet harkar cikin gida ce ta kasar Sin, Birtaniya ta ki amincewa da duk wani yukurin neman 'yancin kan Tibet.(Murtala)