Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-15 10:44:17    
An kammala bikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin nasara a Muscat

cri

Jiya 14 ga wata, da misalin karfe 8 da rabi da dare, agogon wurin, mai rike da wutar yola ta gasar wasannin Olympics na karshe, kuma mataimakin shugaban kwamitin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics na Oman Habib Abdulnabi Macki ya kunna wuta a cikin tukunyar wutar gasar wasannin Olympics a lambun shan iska mai suna Al Qurm. Wannan ya alamanta cewar an kammala gagarumin bikin yawo da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing tare da cikakkiyar nasara a birnin Mascut na kasar Oman.

Gaba daya masu rike da wutar yola 80 sun shafe sa'o'i 3 ko fiye suna zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics. Tsawon hanyoyin da aka ratsa da wutar ya kai kilomita kimanin 20. Bayan da aka fara zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics a gidan cin abinci na fadar Al Bustan, bi da bi ne aka ratsa da wutar a kofar Muscat, da fadar Al Alam, da kasuwar Mutrah Souq da dai sauran shahararrun wuraren yawon shakatawa. A karshe, wutar gasar wasannin Olympics ta isa zango na karshe wato lambun shan iska mai suna Al Qurm. Dubun-dubatar mutanen Oman sun hallaru a lambun shan iska, suna kide-kide da raye-raye tare da matukar farin ciki.

Birnin Muscat na kasar Oman zango na 9 ne na aikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing a ketare. Haka kuma, wannan shi ne karo na farko da aka zagaya da wutar gasar wasannin Olympics a kasar Oman cikin tarihi.(Murtala)