---- Naman Akwiya mai dadi na jihar Mongoliya ta gida ba wani abu ne nadiri ga Amurkawa da Japanawa da mutanen Canada da na yankin Hongkong ba. Ya zuwa karshen shekarar bara, yawan rassan kantin cin abinci mai suna Karamin akuya mai kiba na jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta da aka kafa wadannan kasashe da shiyyoyi ya karu har zuwa 12.
Ba'idin haka kuma, yanzu jihar Mongoliya ta gina tana nan tana ta fitar da naman shanu, da riguna masu gashin tumaki, da karafa, da karafan da ba a samun su sai nadiri, da manyan motoci zuwa kasashen waje.
Mr. Lv Erxi, shugaban hukumar kasuwanci ta jihar Mongoliya ta gida ya bayyana cewa, bayan da aka fara yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen wajen, kuma bisa bunkasuwar tattalin arzikin da aka samu da sauri, jihar Mongoliya ta gida tana ta kara samun suna da sauri wajen kayayyakin da ta fitar zuwa kasashen ketare. Ya zuwa karshen shekarar da ta wuce, yawan masana'antun jihar da suke dukufa kan cinikin waje ya riga ya karu zuwa 3,861, wadanda suke yin ciniki a tsakaninsu da kasashe da shiyyoyi 153 na duniya.
Bisa muhimman tsare-tsaren da aka tsayar na bude kofa ga arewacin kasar, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, jihar Mongoliya ta gida ta samu babban ci gaba wajen cinikin waje, yawan kudin da aka samu wajen cinikin ya karu a kowace shekara. Bisa kididdigar da aka yi an ce, jimlar kudin da jihar ta samu a shekarar da ta wuce wajen cinikin shigi da fici ta kai dala biliyan 7.74, wato ta karu da ninki 2.2 bisa ta shekarar 2002. Jihar ta samu ci gaba har ta kai matsayi na 5 daga cikin dimbin larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kanta da biranen da ke karkashin gwamnatin tsakiya kai tsaye da ke yammacin kasar Sin.
---- A ran 26 ga watan Maris da safe, an sake bude kofar fadar Potala da ke birnin Lhasa na jihar Tibet inda hasken rana ya yi kal. Bayan mummunan tashin hankalin da aka haddasa a ran 14 ga wata, an rufe kofar ala tilas.
An ce, yawan masu ziyarar da aka karba a ran 26 ga wata a fadar ya kai kusan 100, daga cikin su da akwai masu yawon shakatawa 24, sauransu kuwa mutane masu bin addinin Budda na wannan wuri ne.
Fadar Potala tana kan wani tudun da ke da nisan kimanin mita 2000 daga arewa maso yammacin birnin Lhasa, yau fadar nan ta yi shekaru 1300 da ginawa, ita shahararren gini ne na tsohon zamanin kasar Sin, kuma muhimmin sashen kayayyakin tarihi ne da ya samun kariya daga duk kasar Sin.
|