A ran 13 ga wata da yamma, an mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Dar es Salaam, babban birnin kasar Tanzania, wanda ya zama tasha ta 8 da ake mika wutar yola a kasashen waje, wanda kuma ya zama birni daya kawai na nahiyar Afirka da ake mika wutar yola. A ran nan ne, an mika wutar yola cikin nasara. A cikin wannan yunkuri, zumunci da kuma himma daga jama'ar wurin sun fi burge mu. Wakilimmu na gidan rediyon kasar Sin Mr Xie Yi ya tafi tare da masu dauke da wutar yola har dukkan tsawon kilomita 5.
Da kusan karfe biyu na yamma, baki da suka halarci bikin fara mika wutar yola sun isa tashar jirgin kasa ta birnin Dar es Salaam wadda ta hada da Tanzania da Zambiya. Wadannan baki sun hada da mataimakin shugaban kasar Tanzania Ali Mohammed Sheid, da jakadan kasar Sin da ke kasar Tanzania Li Xinsheng da dai sauransu. Mataimakin shugaban kasar Tanzania Mr Ali Mohammed Shein ya bayyana cewa,
'Jama'a da yawa na kasar Tanzania sun yi maraba da wutar yola ta gasar wasannin Olympics, wannan ya bayyana cewa, kasar Tanzania ta nuna cikakken goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing.'
Da daidai karfe biyu na yamma, a cikin kyawawan kide kide, an kunna wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing.
'A halin yanzu, ina tashar jirgin kasa ta birnin Dar es Salaam wadda ta hada da Tanzania da Zambiya. A bayana, an riga an kunna wutar yola, wato za a fara mika wutar yola ta hanyar jituwa a kasar Tanzania.'
Layi na mika wutar yola ya tashi daga tashar jirgin kasa na Tanzania da Zambiya zuwa filin wasanni na kasar Tanzania, wanda kasar Sin ta taimaka wajen gina shi, tsawonsa ya kai kilomita 5. Yawan masu dauke da wutar yola ya kai 80 da suka zo daga Tanzania da Sin da sauran kasashen Afirka.
Da karfe 4 na yamma na wannan rana, an gama aikin mika wutar yola a hukunce.
'A yayin da mataimakin shugaban zartasrwa na kwamitin kula da harkokin gasar wasannin Olympics ta Beijing Mr Liu Jingmin yake mika wutar yola a hannun magajin garin birnin Dar es Salaam, a yayin da ake sanya wutar a cikin fitila, mutanen wurin sun yi farin ciki kwarai da gaske. Bari mu sake nuna godiya ga dukkan jama'ar kasar Tanzania, da himma da zumunci da abokanta, da kaunarku ga wasannin motsa jiki, da wasannin Olympics ne, mun iya mika wutar yola cikin ruwan sanyi, kuma cikin nasara.'(Danladi)
|