Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-14 16:16:24    
Dan kasar Canada Brain A Hodge, kawun dalibai a birnin Fuzhou na kasar Sin

cri

Malam Brain A Hodge dan kasar Canada ne wanda shekarunsa suka kai 72 da haihuwa a bana. Yanzu shi ne babban darekta na babban kamfanin hada magunguna na kasar Canada da ake kira "Rocky Mountain (Fuzhou) Drug Co. Ltd a Turance. Fuzhou sunan babban birnin jihar Fujian ne da ke a kudu maso gabashin kasar Sin. A cikin shekaru da yawa da suka wuce, Malam Brain ya yi ta kokari sosai wajen kulla hulda a tsakanin kamfanonin kasashen Sin da Canada. Bisa babban taimakon da ya bayar, gwamnatin kasar Sin ta ba shi lambar girmamawa ta amince ta kasar. Bayan aikinsa, Brain ya kan nuna himma ga yin aikin ba da ilmi a kasar Sin. Ya shirya kosa kosai na koyar da Turanci a makarantun birnin Fuzhou da yawa, don kara zurfafa ilmin Turanci na dalibai na kasar Sin. Malam Brain ya ce, yana da aminansa dalibai da yawa. Daliban su kan kira shi da "kawu" don nuna masa aminci. Da Malam Brain ya tabo magana a kan kasar Sin, sai ya bayyana cewa, "a shekarar 1984, na zo kasar Sin a karo na farko. A wancan lokaci, kasar Sin kasa ce mai talauci sosai, kuma ba ta samun ci gaba ba. Amma abin da ya ba ni mamaki sosai shi ne, a lokacin da na sake zuwa kasar Sin a shekarar 1987, na ganam ma idona da manyan sauye-sauye da kasar Sin ta samu a cikin irin wannan gajeren lokaci kamar haka. Zuwa farkon shekarun 1990, halin da ake ciki a kasar Sin ya kara samun kyautatuwa."

Bayan da Malam Brain, manajan sashen Asiya na babban kamfanin R. M Ginseng na kasar Canada ya yi ritaya daga aikinsa, ya sake zuwa kasar Sin a shekarun 1990. Ya sa kafa a jihohi daban daban da ke a bakin teku a gabashin kasar Sin, ya yi bincike sosai a kan kasuwannin sayar da tsiren Ginseng. Daga bincikensa, Malam Brain ya gano cewa, jihar Fujian cibiyar samar da tsiren Ginseng ce a kasar Sin. Bayan haka ya gabatar wa masu hannun jari na kafamanin Canada da shawara kan kafa sansanin samar da Ginseng a jihar Fujian. Bayan da kamfanin Canada wanda ya taba yi masa aiki ya kafa reshensa a jihar Fujian ta kasar Sin, ya tarar da Malam Jiang Shaoshu, babban manaja na yanzu na kamfaninsa wanda ya taimake shi sosai wajen bunkasa harkokin kamfanin. Malam Brain ya bayyana cewa, "babban manajana mai ci wani manaja ne da ya kware sosai wajen aikinsa. Ya yi shekaru 17 yana kula da harkokin kamfani. Ya taimake ni wajen kafa wani rukunin aiki. Yanzu, kamfaninmu ya sayi wani sabon fili don kafa sabuwar masana'anta, kuma mun riga mun sami izni daga gwamnatin wurin don kafa wannan sabuwar masana'anta, mun kammala aikin tsara fasalinta, sa'an nan za mu sami kudin jari nan da nan. Sabo da haka muna da makoma mai kyau sosai a kasar Sin."

Ban da wannan, a cikin shekarun nan da suka wuce, Malam Brain ya yi ta yin kokari sosai wajen sa kaimi ga yin ma'amalar tattalin arziki a tsakanin Sin da Canada, kuma ya nuna himma ga kulla hulda a tsakanin kamfanonin kasashen biyu. Yanzu, ya zama mataimakin shugaban kungiyar hadin kan masana'antu masu jarin waje a birnin Fuzhou, da mai ba da shawara ga gwamnatin birnin. Bisa matsayinsa, ya kan gana da shugabannin birnin, ya gabatar musu shawarwarinsa a kan yadda birnin zai kara jawo kudin jari daga kasashen waje. A duk lokacin da 'yan kasuwa na kasashen waje suka zo birnin don binciken harkokinsu, hukumar birnin ya kan gayyaci Malam Brain don gana da su. A lokacin ganawar, ya yi musu bayani a kan birnin Fuzhou da kuma damar zuba jari. Ya kara da cewa, "abin da nake ji a rai, ni mazaunin birnin Fuzhou ne. Kamfanina yana birnin Fuzhou haka kuma iyalina ma a Fuzhou. A ganina, a lokacin da nake zama a Fuzhou, wajibi ne, na yi kokari sosai wajen ba da taimako ga birnina. Sabo da haka na yi farin ciki sosai da zama mai ba da shawara ga hukumar birnin." (Halilu)